Ma’aikatan WAEC za su yi zanga-zanga kan matsalolin walwala

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatan Hukumar Shirya Jarrabawa ta Makarantun Yammacin Afirka (WAEC), sun shirya gudanar da gangamin gama-gari na kwana uku bisa zargin ayyukan ƙwadago na rashin adalci, matsalolin hanyoyin ɗaukar aiki da wasu lamuran da suka shafi walwala acikin hukumar.

Ƙungiyar Ma’aikatan da ba Malamai ba da wasu Cibiyoyi (NASU) ce ta shirya zanga-zangar, wanda tuni aka tsara farawa a ranar 13 ga watan Mayu, 2026 a Hedikwatar WAEC da ke Yaba a Jihar Legas da kuma ofisoshinta na rassan jihohi a Nijeriya.

Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana biyu da WAEC ta sanar da shirinta na gudanar da jarrabawar WASSCE bisa tsari kuma a zamanance ga ɗalibai guda 1,959,636 a makarantun sakandare guda 24,207 da ke sassan Nijeriya.

A wata wasiƙa zuwa ga Shugaban babban ofishin WAEC, Dakta Amos Dangut, NASU ta zargi hukumar gudanarwar hukumar da yin ayyukan da suka saɓa wa doka da cin amanar aiki.

Daga cikin koken da ta lissafo akwai dakatar da shirin ƙara wa ma’aikata matsayi, gabatar da tsarin biya na minimum net pay, ɗaukar matakin hukunta ma’aikata da dai sauransu.

By Babaji