Daga JOHN D WADA a Lafia
Shugaban jam’iyyar Nigeria Democratic Congress [NDC] a jihar Nasarawa Hon. Dogo Shammah ya ce a yanzu haka jam’iyyar ta samu bunƙasa da farin jini cikin lokaci ƙalilan inda a yanzu tama zama babbar jam’iyyar adawa a fadin ƙasar nan.
Ya faɗi hakan ne a jawabinsa a lokacin wani babban zaman hulɗa da ‘yan takara a inuwar jami’iyyar da sauran masu ruwa da tsakinta na yankin Arewa ta tsakiya wanda aka gudanar a Lafia babbar birnin jihar ranar Juma’a.
A cewarsa kasancewar wakilai daga jihohi shida na yankin Arewa ta tssakiyar da babban birnin tarayya Abuja da jam’iyyar ke cigaba da samu ne ke ƙara gudun da sabuwar jam’iyyar ke yi a yanzu.
Shugaban NDC na Nasarawar Hon. Dogo Shammah ya kuma ce ko da yake Nigeria Democratic Congress ɗin sabuwar jam’iyya ce amma shugabanninta da magoya bayanta ba sababbi ba ne ga buri da muradin al’ummar Najeriya.
Hon. Shammah yace a yanzu jam’iyyar na tsara kanta a matsayin jagorar adawa gabanin zaɓen 2027 a jihar Nasarawa da faɗin ƙasar baki ɗaya.
Yace abin da ya bambanta NDC da sauran jam’iyyu shi ne samun jagoranci mai tsayawa kan gaba wanda ya dogara kan ladabi da adalci da gaskiya da amana a dukkan matakai tare da niyyar ƙwace mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a 2027.
A cewarsa NDC na samun shigowar manyan ‘yan adawa da manyan ‘yan siyasa waɗanda suka himmatu wajen ceto ƙasar daga rashin gudanarwa mai kyau na gwamnatin tarayya ƙarƙashin APC ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa a inuwar ta wato sanata mai daraja Seriake Dickson.
Ya buƙaci shugabannin jam’iyyar a faɗin jihohi da su jajirce wajen ƙarfafa jam’iyyar yana mai cewa ‘yan Najeriya na neman shugabanci mai gaskiya da ke kula da al’umma kuma madadin hakan shi ne Nigeria Democratic Congress.
Shugaban ya ce NDC ita ce kaɗai dandali da ke da karfi da ƙudiri na kawo cigaban gaske ga yankin Arewa ta tsakiya da yaƙi da rashin tsaro da juyar da yanayin koma bayan tattalin arziki tare da samar da mafita ga ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar.
Daganan sai yayi amfani da damar inda yayi kira na musamman ga wakilan da suka halarci taron da su gudanar da siyasa mai ɗorewa wadda za ta jawo hankula da tunanin al’umma kana ya buƙaci jam’iyyar da ta fito da ‘yan takara masu gaskiya waɗanda za su iya lashe zaɓe a dukkan matakan mulki.
