Abin Al-ajabin Zazzau: Mahmud Sadis ya janye batun shiga takarar kujerar Majalisar Wakilai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mahmud Sadis Buba da aka fi sani da Al-ajabin Zazzau, ya janye batun shiga takarar kujerar Majalisar Wakilai ta mazaɓar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.

A wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban jam’iyyar APC na jihar, wadda kuma ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook a ranar Asabar, Buba ya ce ya ɗauki matakin ne cikin mawuyacin hali, wanda ya biyo bayan shawarwari da masu ruwa da tsaki, yana mai cewa ya yi haka ne domin maslahar jam’iyyar da kuma al’ummar mazaɓar tasa.

Ya kuma yaba wa Gwamna Uba Sani na Kaduna da jagorancin APC bisa ba shi damar neman shiga takarar a karon fari.

Abin Al-ajabin ya bayyana cewa ya gamsu da matakin tare da yi wa mazaɓar da al’umma godiya bisa samun goyon baya cikin harkokin siyasarsa tun daga farko har zuwa yanzu.

Haka kuma, ya ce zai cigaba da yin biyayya ga APC tare da zama mai sadaukarwa a gare ta, yana mai jaddada cewa matakin nasa ba alamar gazawa ba ce, saidai abu ne da aka yi don ciyar da jam’iyyar gaba.

Kazalika, ya tabbatar da cewa zai cigaba da aiki tuƙuru a matsayinsa na mamban jam’iyya domin samun nasara ga ɗan takarar da jam’iyyar ta fitar yayin babban zaɓen 2027.

Har ila yau, ya kirayi magoya bayansa da su kwantar da hankali tare da kasancewa cikin haɗin kai da miƙa wuya ga matakan jam’iyyar musamman wajen ba ‘yan takarar da ta tsayar goyon baya.

A ‘yan kwanakin nan ne aka shiga cece-kuce akan sahihancin shekarunsu, inda wasu ke iƙirarin 16 ne yayin da shi kuma ya ce ya kai 30 a hira da wata kafar labarai ta yi da shi.

By Babaji