
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mohammed Bello, wato ɗan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya zargi jami’an Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) da hana ganin mahaifinsa domin ba shi kulawa ta ‘yan uwantaka yayin yake tsare.
Wannan zargi na ƙunshe ne a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a ranar Asabar, inda ya bayyana matakan hukumar a matsayin “babban farmaki” akan ‘yancin mahaifin nasa.
Tun a ranar 19 ga watan Fabarairu, 2026 ne El-Rufa’i yake tsare a hannun ICPC bisa zarge-zargen badaƙalar wasu maƙudan kuɗaɗe da aka danganta masa a lokacin da yake gwamnan Kaduna daga 2015 zuwa 2023.
A baya dai an ba tsohon gwamnan hutun wucin-gadi domin samun damar halartar gudanar da jana’izar mahaifiyarsa da ta rasu.
Da yake tsokaci akan al’amarin, Mohammed Bello ya zargi ICPC da bijire wa umarnin kotu na hana likita na musamman ganin mahaifin nasa.
Ya kuma zargi hukumar da hana abokiyar zaman mahaifiyarsu, wato Aichatou El-Rufa’i ganin mijinta a lokacin da ta kai masa abincin dare.
Ɗan tsohon gwamnan ya bayyana waɗannan matakai a matsayin karan-tsaye ga dokokin ƙasa da na ‘yancin ɗan-adam, yana mai cewa ba za su cigaba da lamuntar wulaƙanci ba da sunan aiki a hukumance daga ɓangaren jami’an hukumar.
A shekarar 2024 ne majalisar dokokin Kaduna ta zargi El-Rufa’i da hannu a karkatar da Naira biliyan 423 na gwamnatin jihar, inda ta buƙaci hukumomin yaƙi da rashawa su gudanar da bincike akansa.
