Zaɓen fidda gwani na APC: Hamza Sule Faskari zai yi takarar majalisar wakilai a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC ta tabbatar da takarar Hamza Sule zai wakilci alummar ƙananan hukumomin Faskari,Kankara da Sabuwa a zauren majalisar wakilai a zaɓen 2027.

Bikin jaddada takarar da ya gudanar a Ƙankara da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyar sun yaba da yadda kwamitin sasancin ya gudanar da aikin sa.

Shugaban kwamitin sasancin Injiya Tanimu Sabuwa ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyar da suka fito daga mazaɓu 31 na ƙananan hukumomin Faskari, Ƙankara da Sabuwa wanda suka wakilci ɗaukacin ya’yan jam’iyar suka tabbatar da takarar Hamza Sule.

Ya ce wasu abubuwan da akai la’akari da su su ne farin jini da son alumma na ɗan takarar,da kuma karɓuwa ga alumma da ƙarfin siyasar sa.

“Babu shakka Hamza Sule zai wakilci alummar sa ya kuma kawo wa jam’iyar APC farin jini da suna idan ya shiga majalisar wakilai ta ƙasa,”inji shugaban kwamitin.

Da yake jawabi mataimakin gwamnan jihar Farouk Lawal Jobe ya yabawa kwamitin sasancin ƙarƙashin tsoton mataimakin gwamnan jihar Alhaji Tukur Ahamed Jiƙamshi kan yadda suka gudanar da aikin su ,sai yayi kira ga waɗanda suka faɗi zaɓen da su zo a haɗa kai domin samun nasara a zaɓen 2026 mai zuwa.

Da yake jawabi zaɓaɓɓen ɗan takarar Hamza Sule ya gode wa masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC a yankin da suka ga dacewar sa na wannan takarar.

Sai yayi kira ga ya’yan jam’iyar da su haɗa kai da kuma tabbatar da waɗanda basu yanki katin zaɓe ba da su hanzarta yi.

Hamza Sule ya Kuma yi alƙawarin da zaran an zaɓe shi zuwa majalisar wakilai zai mai da hankali wajen inganta tsaro da ƙara kawo jami’an tsaro da kayan aiki a yankin.

Hamzu Sule ya riƙe mukamin kwamishinan muhalli da na albarkatun ruwa ya na kuma rike da sarautar Wamban Faskari kuma Sadaukin ƙasar Hausa wanda da yawa jama’a ke bayyana a matsayi mutumin kirki ga taimakawa mutane.

By ukarofi