Tsohon ɗan takarar gwamnan Bauchi, Air Marshal Sadique ya yi ritaya a siyasa

Spread the love

Tsohon ɗan takarar gwamnan a Jihar Bauchi a zaɓen 2023 kuma tsohon Hafsan Sojin Sama na Nijeriya, Sadiq Baba Abubakar, ya sanar da janyewarsa daga harkokin siyasa.

Rahotanni sun bayyana cewa Air Marshal Sadiq Baba Abubakar mai ritaya ya ɗauki wannan mataki ne sakamakon sauye-sauyen da ke faruwa da kuma rikice-rikicen da suka dabaibaye Harkokin jam’iyyun siyasa a ƙasar nan a baya-bayan nan.

Tsohon Shugaban rundunar sojin saman ya kasance ɗan takarar gwamna a Jihar Bauchi a zaɓen 2023, Inda ya taka muhimmiyar rawa a fafatawar siyasar jihar tare da jan hankalin jama’a da dama.

Majiyoyi sun ce ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda harkokin siyasa ke tafiya a halin yanzu, musamman rikice-rikicen cikin gida da sauye-sauyen da ke faruwa a jam’iyyun siyasa daban-daban.

By Babaji