Sun faɗa wa Tinubu wai ina son halaka shi saboda mulki, inji Shettima

Spread the love

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa wasu mutane sun yi ƙoƙarin haddasa saɓani tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu watanni uku kacal bayan hawansu mulki.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Yakubu Gowon, mai taken “My Life of Duty and Allegiance”.

A cewarsa, wasu mutane daga jihar Borno da bai ambaci sunayensu ba sun je wajen Tinubu suna zarginsa da cewa yana shirin kashe shugaban ƙasar domin ya karɓi mulki.

Ya ce, Tinubu ya kira shi tare da gaya masa cewa wasu mutane sun zo suna masa ƙorafin cewa ya daina sanya tufafin da Shettima ke ba shi.

Ya ce shugaban ƙasar ya yi watsi da zargin bayan ya lura cewa labarin bai da tushe, domin tun kafin zaɓe ne Shettima ya ba shi tufafin, a lokacin da har yanzu shi ɗan takarar shugaban ƙasa ne.

“Sun ce bayan zaɓe ina shirin amfani da tufafin wajen kashe shi domin na karɓi mulki. Amma shugaban ƙasa ya ci gaba da sanya tufafin saboda ba mutum ne mai yarda da tsafe-tsafe ba,” in ji Shettima.

Kazalika, Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rungumi haɗin kai tare da zama masu taimakon juna maimakon haddasa rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.

By Babaji