Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani mummunan harin da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai a wasu ƙauyuka da makarantu da ke ƙaramar Hukumar Orire a Jihar Oyo ya jefa al’umma cikin tsananin tashin hankali, bayan da aka yi awon gaba da malamai da zalibai 46, ciki har da wata yarinya ’yar shekara biyu.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda maharan suka mamaye makarantar Community High School Ahoro-Esinele da kuma makarantar Yawota Baptist Nursery and Primary School, kafin su tafi da mutane da dama zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Shugabannin al’umma a yankin sun bayyana cewa daga cikin mutanen da aka sace akwai malamai bakwai da ɗalibai 39, mafi yawansu ƙananan yara masu shekaru tsakanin biyu zuwa 16.
ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi tayar da hankali shi ne yadda wata yarinya mai suna Christianah Akanbi mai shekara biyu kacal ta kasance cikin waɗanda aka yi garkuwa da su daga makarantar Yawota Baptist Nursery and Primary School.
Bayan harin, mazauna yankunan sun shiga cikin firgici da jimami, yayin da iyaye da ’yan uwa ke ci gaba da zaman ɗar-ɗar kan makomar ’ya’yansu da ‘yan uwansu da aka sace.
Cikakken bayanin malaman da aka sace:
Shugabannin al’umma sun tabbatar da cewa malamai bakwai da aka yi garkuwa da su sun haɗa da:
Misis Alamu Folawe – Shugabar makarantar Community High School Ahoro-Esinele.
Mista Ojo Jonathan – Mataimakin shugaban makaranta.
Mista Olatunde Zacchaeus – Malami.
Mista John Olaleye – Malami.
Mista Michael Oyedokun – Malami.
Misis Oladeji – Malama.
Mary Akanbi – Malama a makarantar Yawota Baptist Nursery and Primary School.
Rahotanni sun nuna cewa malamai da ɗaliban suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum ne kafin maharan su kai farmaki cikin gaggawa.
ɗaliban da aka sace daga Ahoro-Esinele:
Waɗanda aka yi garkuwa da su daga yankin Ahoro-Esinele sun haɗa da:
Rashida Tajudeen mai shekara 11, Ahmed Ramoni mai shekara 8, Abdulsalam Toyib mai shekara 4, Baraka Abioye mai shekara 16, Fatimo Jimoh mai shekara 15, Hassan Azeez mai shekara 14 da Joshua Adeleke mai shekara 13.
Waɗanda aka sace daga ƙauyen Yawota:
Daga ƙauyen Yawota kuwa, maharan sun yi awon gaba da Samuel Oyedele mai shekara 7, Emmanuel Oyedele mai shekara 4, Idowu Taiwo mai shekara 4, Christianah Akanbi mai shekara 2, Juwon Sunday mai shekara 7, Sikiru Salami mai shekara 3, Soliu Salami mai shekara 4, Ojo Joseph mai shekara 8, Lydia Adewole mai shekara 8, Testimony Jacob mai shekara 5, Kehinde Kaosara mai shekara 7, Sewa Seyi mai shekara 7, Waliya Bello mai shekara 4, Lydia Olohunloluwa mai shekara 7, Damilare Oderinde mai shekara 8, Deborah Adebowale mai shekara 5, Aisha Oguntowo mai shekara 10, Lege Taiwo mai shekara 12, Balkis Ayanwale mai shekara 8 da Asa David mai shekara 10.
Waɗanda aka sace daga Oniya da Alawusa:
A ƙauyen Oniya kuwa, an sace Shuaibu Aliyu mai shekara 10, Ahmed Aliyu mai shekara 7, Muiz Aliyu mai shekara 5 da Jomiloju Ogunlola mai shekara 6.
Haka kuma daga ƙauyen Alawusa, maharan sun sace Agune Noah mai shekara 8, Elizabeth Abadi mai shekara 5, Tosin Abadi mai shekara 9, Pius Stephen mai shekara 5, Hannah Ojo mai shekara 14, Habidat Ayanwale mai shekara 7, Mary Gabriel mai shekara 6 da Jacob Gabriel wanda ba a bayyana shekarunsa ba.
Baya ga sace mutane, shugabannin yankin sun ce maharan sun ƙwace babura huɗu daga hannun mazauna yankin, uku daga ƙauyen Yawota da ɗaya daga makarantar sakandaren Ahoro-Esinele.
Bayan harin, malamai a yankunan da abin ya shafa sun dakatar da zuwa makaranta saboda fargabar tsaro, yayin da suke kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatin Jihar Oyo da su gaggauta ɗaukar matakan ceto waɗanda aka sace.
Sun bayyana cewa ci gaba da kai hare-hare makarantu na jefa rayuwar yara cikin haɗari tare da lalata harkar ilimi a yankunan karkara.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da harin tare da tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su yi duk mai yiwuwa domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Haka kuma Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya fuskanci kira daga mazauna yankin da su ƙara tsaurara matakan tsaro domin hana sake aukuwar irin wannan hari.
Lamarin ya sake bayyana irin yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da shafar makarantu da rayuwar yara a Nijeriya, musamman a yankunan karkara da ke fama da hare-haren masu ɗauke da makamai.
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun bayyana cewa hare-haren makarantu na iya ƙara haddasa koma baya ga ilimi, tare da jefa iyaye cikin fargabar tura ’ya’yansu makaranta.
Har yanzu babu wani cikakken bayani daga hukumomin tsaro kan inda aka kai waɗanda aka sace, yayin da iyalai da al’umma ke ci gaba da addu’o’i da jiran samun labarin ceto su lafiya.
