Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Wani rahoto da kafar watsa labarai ta Arewa Updates ta wallafa game da wani malamin Islamiyya da aka kama kuma ake zargi da lalata da wasu ƙananan yara mata su huɗu, dake karatu a makarantar da yake koyarwa a garin Inusawa, a Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano, ya yi matuƙar tayar min da hankali. Sakamakon irin takaici da abin tausayi da ke cikin wannan labari. Kodayake kawo lokacin rubuta wannan rahoto, rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama wannan baragurbin malami, ana bincike kan anin da ake zarginsa a kai.
Ba tun yanzu ba ake samun rahotanni iri-iri da suka shafi cin zarafin yara ’yan makaranta daga malaman da aka bai wa amanarsu. Nasan ba za mu manta da kisan gillar da aka yi wa Hanifa ba,
wata yarinya ’yar shekara 5 da shugaban makarantar su ya yi garkuwa da ita kuma ya kashe ta daga baya. Idan kun tuna lamarin ya faru ne a yankin Nasarawa na Jihar Kano, a ranar 2 ga watan Disamba na shekarar 2021.
Kodayake wata kotu a Jihar Kano ta yankewa malamin da ya yi wa Hanifa wannan ɗanyen aikin da sauran waɗanda ke da hannu a kisan gillar, hukunci mai tsanani. Amma da alamun hakan bai zama darasi ga wasu ɓatagarin malamai ba, waɗanda suke cigaba da gurɓata rayuwar wasu yara da ke koyon ilimi da tarbiyya a ƙarƙashin kulawarsu.
Ba za mu manta da labarin wani malamin makaranta mai shekaru 19 a Abuja ba, wanda ya yi wa wani ɗalibi mai shekaru 9 fyaɗe ta hanyar luwaɗi. Shi ma dai daga baya rahotanni sun nuna cewa wata Babbar Kotu a Abuja ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. An bayyana cewa, a ranar 19 ga watan Maris na shekarar da ta gabata, malamin ya aika a nemo masa ɗalibin bayan an tashi a makaranta, daga nan kuma sai ya ja shi wani waje a cikin daji ya yi masa fyaɗe. Wannan hukunci ya zo daidai da abin da ya faru da wani malamin makaranta mai shekaru 41 da ya yi wa wata ƙaramar yarinya mai shekaru 6 fyaɗe a makarantar da yake koyarwa, a yankin Omole dake Legas.
Abin farinciki ne yadda ake samun kotuna suna hukunta waɗanda ake samu da wannan laifi, idan har an tabbatar da laifin da ake zargi a kansu. Sai dai inda abin haushi da takaicin yake shi ne inda iyaye da ýan’uwa za su haɗu don a kashe maganar saboda kada labarin abin da ya faru ya watsu har a tona asirin yarinya ko yaron, ta yadda mutane za su fara tsangwamar su.
A sanadiyyar aikin da nake yi na taɓa cin karo da wani rahoto da aka sa ni aiki a kai a garin Gombe, inda wasu samari biyu ’yan gida ɗaya suka yi wa yara ’yan mata su uku ’yan uwan juna fyaɗe, sakamakon zaman maƙwaftaka da suke yi. Hakan ya faru ne a dalilin ƙorafin da yaran matan suka yi kan cewa yaran maƙwaftansu da suke shiga suna koya musu karatu suna yunƙurin ɓata musu rayuwa a lokuta daban-daban. Wannan ya haɗa har da zargin da ake yi wa wani dattijo mai kimanin shekaru 50 wanda ke sana’ar wankin hula a shagon dake jikin gidan da yaran matan suke, wanda yake leƙensu a bayan gida, yana ƙoƙarin yaudarar ƙananan yaran gidan mata don ya yi lalata da su a shagonsa.
Irin waɗannan labaran marasa daɗin ji suna nan da yawa, ba kawai a Kano, ko Gombe ba, kusan a ko’ina a ƙasar nan. A lokuta da dama hukumomi ba sa samun labarin abubuwan dake faruwa har sai labari ya watsu sosai, sakamakon yadda iyaye ke ƙoƙarin ɓoye irin waɗannan abubuwa marasa daɗi da suka faru da yaransu. Wani lokacin kuma su yaran ne ke ƙoƙarin ɓoye wa iyayensu, irin waɗannan abubuwa don fargabar iyayen za su tuhume su da dalilin da ya sa suka kusanci waje kaza ko suka je waje kaza tare da wane, har wani abu ya faru.
Lallai ya kamata mu sa ido sosai kan rayuwar yaranmu, mu ba su dukkan kulawar da suke buƙata, tun daga tasowar su, tsaron lafiyarsu, da mutuncinsu, ingancin iliminsu, da walwalar su. Yana da kyau mu saki jiki da su yadda za su kusancemu su yi mana bayanin abubuwan da ke faruwa da rayuwarsu. Ba lallai sai mun zauna mun wuni a gida ko mun ware masu rana ta musamman ba, amma lallai mu riƙa nuna damuwa da kulawa ga duk wani abu da ya shafe su. Mu zama abokan shawararsu, don idan sun fahimci suna iya samun aminci da natsuwa a tare da mu to, ba za su riƙa ɓoye mana komai ba. Lokaci zuwa lokaci mu riƙa samun dama ko da aƙalla sau ɗaya ne da za mu ci abinci tare da su, ko da ba a kwano ɗaya ba, ya zama dai a muhalli ɗaya. Mu kuma riƙa samun lokaci muna fita da su zuwa ziyara gidajen ’yan uwa, da wuraren shaƙatawa, don sanya musu walwala da nishaɗi a ransu.
Ina fatan hukumomin da abin ya shafa za su yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a sassan ƙasar nan da suka shafi cin zarafin ƙananan yara maza da mata, rashin tsaro, yunwa da talauci da yawaitar yara ’yan gudun Hijira a sansanoni babu kyakkyawar tarbiyya babu kulawa, da shigar yara ƙanana ƙungiyoyin asiri da ta’addanci. Lallai gwamnati ta yi ƙoƙari ta tabbatar da ganin ana hukunta masu cin zarafin yada, da ɗaukar matakan da suka dace na kyautata makomar yara da tsare martabar su.
