Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Cikin wani ‘forum’ ɗinmu mai suna “Amsoshin Tambayoyin Ilhadi” sai wani Hussein Abdool daga ƙasar Nijar ya jeho wannan tambaya: “Musulmi suna yin da’awar cewa komi akwai abinda ya samar da shi. Tambaya: To, shi Allah mi ya samar da shi?”
Wannan tambaya ce da aka dade ana yinta tsawon tarihi, musamman daga Mulhidai da ma wasu masu imanin, abinda ya sa Allah cikin Qur’ani ya saukar mana da “Lam ya lid, wa lam yulad” wato bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba.
Kafin nan muna iya tunawa da Lamarudu, kamar yadda labarin ya zo cikin Bible da Qurani yadda ya kalubalanci Annabi Ibrahim cewa shi ma Allah ne matukar cewa siffar Allah ta azurtawa da rayawa ce to shi ma yana azurtawa da rayawa, yadda ya azurta wani talaka kuma ya saka a ka saki wanda aka yankewa hukuncin kisa. Kafin Ibrahima ya kure shi da cewa to Allah ke fito da rana daga gabas ta fadi yamma.
A wannan zamani namu, akwai manyan mulhidai, irinsu Dawkins da Kraus da ma wasu yaranmu a nan Arewacin Najeriya da ke inkarin samuwar Allah sai su ke irin wannan tambaya cewa wanene ya halicci Allah kansa. A yanzu mulhidai na amfani da kimiyyar zamani a matsayin makami da zasu rudar da mutane, kuma abin takaici yakin nasu na yin nasara sannu-sannu.
Ba nufi na ba ne, na kawar da mulhidai daga akidarsu, sai dai haskawa matasa su gane wannan illar.
Kamar yadda kakanmu Annabi Ibrahim ya ke amfani da basira da nassi wajen wa’azi, ta haka ne kawai za mu iya murkushe wannan annoba. Don haka muna da hanyoyi uku da zamu iya nuna wofintar tambayar cewa wa ya halicci ubangiji. Wato ta hanyoyin hikima, falsafa da kimiyya.
A hankalce, idan zamu dauki misalin cewa yaro ya yi fitsari a wandonsa, wandon zai jike kuma idan ka taba wandon za ka ji danshi ko? Idan ka tambayi daga ina aka sami danshin za’a ce maka daga fitsarin ne. Shi kuma fitsarin daga ruwan da yaron ya sha, kaga danshi ya dogara ne daga ruwa ko? Amma za ka iya tambayar cewa daga ina shi kuma ruwan ya sami danshin sa?
Ko kaɗan, domin danshin ba siffar ruwa ba ce halayya ce. Tamkar haka ya sa ba za ka iya cewa wanene ya halicci Allah ba domin shi kadai ne ya iya kirkirar halitta kuma ya tsara halitta yadda idan ba shi ba, babu wanda zai iya halittawa. Idan akwai mai inkarin haka, sai Allah ya kalubalance shi a Qurani da cewa: Q22:73 “”Ya ku mutãne! ga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru (gaba dayansu) gare shi.”
Idan ka ce akwai mai halitta ba Allah ba, to kawo shi ya halicci ‘Kuda” kawai. Babu mai iya yin haka daga nan har tashin kiyama saboda Allah kadai ke iya halitta ba mai iya halitta wani abu ballantana ya halicci mai halittawa.
A kimiyance, idan muka duba zamu ga cewa kwayar halittar gado, wato DNA idan da za a ce tsautsayi zai iya samar da guda daya wanda sinadirai 2000 (enzymes) ne suke harhaduwa bisa wani tsari mai oda, to kafin tsautsayi ya iya hada su yadda Allah ya jera su sau daya sai an gwada sau adadin 100000000000000000000000000000000000000000. Wannan adadi (zero 40) ba shi da suna sai dai mu kira shi malala malala, domin ba gashin tinkiya ba hatta kwayar tsakuwa, digon ruwa, taurari da dabakoki kaf ba su kai wannan adadi ba.
Shi ya sa ba na mamakin ganin yadda tsawon dubban shekaru Dan Adam ya kasa gano sirrin Rai. Masana kimiyya irinsu Francis Crick da Stanley Miller sun shafe gwamman shekaru a dakin gwajin kimiyya ko zasu iya samar da kwayar halitta mai rai (Cell) amma sun gaza ba tare da samar da abinda ya wuce sinadaran Amino Acid ba, wato tubalin da ke gina kwayar halitta mai rai. Don haka kirkirar halitta abu ne da ba wanda zai iya samar da ita sai Allah, mahaliccinta, kuma kimiyya ta mika wuya.
Sannan mulhidai a wannan zamani, sun kwace nazariyyar asalin halitta (Evolution) tare da mata kwaskwarima yadda zata nuna cewa ai babu wanda yayi halitta, wato halitta ta samar da kanta ne. Amma abinda mutane ba su sani ba shine cewa shi wanda ake alakantawa da nazariyyar, wato Charles Darwin, ba Mulhidi ba ne kuma har ya mutu ya yarda da Allah abinda ya bayyana karara cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “Life and Letters”. Kuma ko a cikin gagarumin littafinsa wanda ya wallafa bincikensa “On the origin of species” bai tabo asalin samuwar halitta ba sai dai daga bayan samuwarta yadda ta wanzu a doron kasa kuma ta yadada. Amma bayan mutuwarsa, Mulhidai sun dauki nazariyyarsa suke nuna cewa halitta ba wanda ya yi ta, ta samar da kanta ne da kanta.
Wani masanin kimiyya, Fred Hoyle, a shekarar 1952, ya gano wani tsarin daidaito a kwayar zarra ta Carbon (wadda ita ce ginshikin wanzuwar jikuna masu rai). Wannan kwayar zara na da wani daidaito wanda ke nuna cewa idan da daidaiton ya gaza da kashi 4% kacal, to da duk kwayoyin zarra na Carbon ba zasu samu ba. Kun ga da mu kanmu ba mu samu ba kenan. Wannan bincike ya sa masana tsunduma cikin wannan fage, ilai kuwa sai gashi sun gano wasu tsarukan na daidaito (abinda ake kira da Anthropic Principle).
Tashin farko ita kanta Big Bang, wato haihuwar wannan sammai da kassai ta mu (wadda Allah ya mana bayani a Suratul Anbiya aya ta 30) an gano cewa, da a dakika guda bayan fashewar, da a ce saurin fadadar sammai ya gaza da kaso guda cikin wata lambar mai malala-malala (wato 1 da sifili guda sittin a bayanta) da samman ta koma ta sake dunkulewa. Haka nan akwai ginshikan dokoki hudu (Fundamental forces) wadanda ke dauke da duk wata halitta, walau mai rai ko mara rai;
1. Nukiliya mai karfi (Strong nuclear force) wanda shine ya ke zaunar da yayan kwayar zarra a dunkule cikin tsakiyar kwayar zarra, wato Atom (kwayar zarra kuma ita ce tubalin ginin kowane irin jiki, mai rai da mara rai).
2. Nukiliya mai rauni (Weak nuclear force) wanda shi ne ke saka rubuwe (radioactive) ta ƙwayar zarra.
3. Lantar-Maganadisu (Electromagnetism) wanda shine ginshikin sufuri na lantarki da magandisu da ke daukar haske, kuzari da su radio, x-ray, infrared, microwave da sauransu.
4. Maganadisu (Gravity) wanda shine ginshikin motsin jikuna kama daga manyan dabakoki, taurari da duniyoyi da abinda ke cikinsu har zuwa kan kwayar zarra.
Duk wadannan dokokin, Allah ya saita kowanne iya wani geji wanda a misali Idan da a ce nukiliya mai karfi ya yi rauni daga gejinsa, to da babu wata kwayar zarra banda ta Hydrogen da zata iya samuwa. Idan kuma da nukiliya mai rauni karfinsa ya wuce yadda ya ke to da duk Hydrogen ta zama Helium. Haka nan shi ma Lantar-maganadisu da karfinsa ya fi yadda ya ke to da duk kwayoyin zarra zasu dunkule yadda ba zasu iya ta’ammali da wasu kwayoyin zarra wajen auratayya domin samar da wasu gungun sinadarai ba. Da kuma karfin Lantar-maganadisu ya gaza yadda ya ke, hakika da kwayoyin zarra sai su yi ta rubewa. Yanzu wannan tsarin ne zaka ce katsam ya samu babu wanda ya samar da shi?
Mulhidanci, addinin shaidan ne da ke kokarin yin amfani da kimiyya ta karya (Pseudo-science) domin dulmuyar da matasan mu. Sun cusa abin cikin hikima da wayo yadda suka mamaye bangarorin nazariyyar kimiyya da nazarinta inda suka dauki wancan bincike na Darwin akan asalin halitta suka kafirtar da shi. Hakika sun kafirtar da shi ne, domin sama da shekaru 600 kafin Darwin, malaman Musulunci fitattu guda uku sune suka fara gano yadda tsarin yake sakamakon umarnin Allah da ya ce; Q29:20 “Ka ce: ”Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa’an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin halitta.”
Don haka Al Haytham cikin littafinsa “Kitabul Manazir” da Al Biruni cikin littafinsa “Kitabul Jamahir” da kuma Ibn Khaldun a nasa littafin “Al Muqaddima” duk sun kawo nazariyar asalin halitta. Amma barcin da musulmi su ka yi da daina binciken ilimi sai turawa su ka sace ilimi gabaɗaya.
Bayan Darwin ya buga tasa nazariyyar, sai wasu mulhidai karkashin jagorancin Thomas Huxley su ka karkata akalar binciken da lullube shi cikin mulhidanci tare da kwaikwayar tsarin addini a fakaice inda suka maida nazariyyar tamkar Bible dinsu, tare da dauke duk wani quality na ubangiji su ka mayar wa “Nature” tare da samar da mujalla mai suna Nature ta zama kakakinsu. Sun maida jami’o’i tamkar masallatansu inda suke daukar malaman kimiyya domin koyar da mulhidanci da sunan kimiyya. An fitar da tsarin wallafa bincike (peer review) yadda ya zama tsarinsu na wa’azi yadda sai wanda su ka aminta da shi zai samu sahalewar a buga bincikensa kuma yada shi. Ta haka ake samar da mabiya sabbi sannan manyan annabawansu su ne irinsu Dawkins da Krauss da ke kira zuwa ga addinin ta hanyar wa’azi a littafansu da lakcoci.
A bayyane ya ke cewa Dan Adam ya gaza wajen ganowa ta hanyar kimiyya ina halitta ta samo asali kuma ina rai ya sami asali. Hatta hankali na gane abubuwa (consciousness) da ni da kai da kowa ke da shi, babu wanda ya san asalinsa. Haka nan a kullum kimiyya dada tabbatar da mahalicci ta ke yi a cikin tsarin halitta. Kafin bayyanar Einstein, sakamakon nazariyyar Darwin da yadda aka lullube ta da mulhidanci hadi da nazariyyar Isaac Newton wanda ya kawo dokokin motsin jikuna (Laws of motion) a karshen karni na 19 sai masana kimiyya masu ra’ayi na mulhidanci suka daga hannu da shewar cewa an ga bayan addini, yadda gagarumin mulhidi dan Jamus Freidrich Nietzsche ya wallafa littafinsa “The Death of God” wato kimiyya ta kashe Allah ba shi da sauran tasiri domin komai a yanzu kimiyya zata iya bayaninsa.
Katsam sai Allah ya jeho Einstein wanda nazariyyarsa ta Relativity ta zo ta yi rugu-rugu da tsarin “Reductionism” cewar kimiyya zata iya bayyana komai. Sai aka gane cewa komai “dan ya danganta ne” da wani abu (wato Relative), wanda kuma ya hade sarari (space) da time cewa a dunkule suke ba daban-daban ba.. Wannan mahanga ta dawo da samuwar Allah cikin tsara halitta, sannan ta karfafa bayan samun nazariyyar Werner Heisenberg wanda ya gano sabuwar dokar da aka kira da “Uncertainty principle” wato dokar “kila-wa-kala” a kimiyya, dokar da hatta shi gwarzon kimiyyar Dan Adam, wato Einstein da kansa, bayan nazarin dokar yadda ta ke, sai da ya shiga rudanin da ya ce “God does not play dice” (wato “Kai, ace Allah zai yi wasan dara?).
Domin abin da dokar kila-wa-kala ta gano shine cewa idan ka yi kokarin auna inda yayan kwayar halitta (wato particle) su ke to ba kuma zaka iya auna gudunsu ba a lokaci guda. Idan kuma ka iya auna gudun to hakika inda su ke zai kauce maka. Babu wato doka a kimiyya da ta tabbatu a zahirance irinta, domin ba gibin iliminmu ne ya sa hakan ba, illa dai yadda Allah ya tsara halittar. Wannan doka (quantum indeterminacy) a yanzu ana amfani da ita wajen kere-keren kwamfuta masu tsananin gudu da sauran abubuwa.
Ya ilahi, idan har ba ka iya gane yaya halitta mara rai ta samu ba, ko yadda rai ya samu, ko kuma ina hankalin gane abubuwa (consciousness) ya me, da hatta yadda tsarin kwayoyin halitta mafi kankanta ke wanzuwa…shine kuma zaka fara giggiwar wai wa ya halicci Allah?
Mulhidai ku ci gaba da wasa kwakwalenku a wadannan abubuwa tukuna kafin gu gaza, domin kimiyya duk ta rufe kofofinsu. Shi wanda kuke inkari shine; Q6:103 “(Ubangijinku shine wanda) Gannai bã su iya riskuwarSa, kuma Shĩ Yanã riskuwar gannai, kuma Shĩ ne Mai tausasãwa, Masani.”
A ƙarshe, kalubalenku malamai, dole ku farka daga barcinku domin cika nauyin da ke kanku. Ilimin kimiyya da falsafa wajibi ne kamar yadda mu ka gani Allah na ta umartarmu a Qurani, sannan mun ga yadda ta hanyar falsafanci Ibrahimu ya wofintar da Lamarudu akan magànar wanene Allah. Kuma kada mu manta Annabi ya umarce mu da cewa “Hikima kayanmu ce, duk inda muka ganta mu dauki abarmu”.
Amma kash! Malamai sun shagala da duniya sai neman arziki da neman girma da kwaɗayi da fada da juna a kan abubuwa marasa mahimmanci. Malamai sun gidadantar da wayayyen addini saboda kyamatar nazari da bincike, sun bige da rigima a kan mabanbantan fatawoyi da bangarancin kungiya. Wannan dalili ya sa matasa a arewa ke zama mulhidai domin malamai ba sa iya basu amsoshin da ke musu yawo a kwakwalwa saboda su kansu malaman sun jahilci al’amuran. Haka nan tsatstsauran ra’ayin addini shi ma ya yi tasiri sosai wajen kore matasa daga addini.
