APC zaɓe ko naɗi?

Spread the love

Da farko, ba na nufin cin zarafi ko tayar da zaune tsaye. Magana ce kawai da ya dace a duba tare da fahimtar inda matsaloli suke.

Tun farko, jam’iyyar APC ta gudanar da zaɓukan fidda gwani na ‘yan takarar Majalisar Wakilai, inda wasu suka yi murna yayin da wasu kuma suka nuna rashin gamsuwa. Haka rayuwar siyasa take. A yanzu haka jam’iyyar na ƙoƙarin rarrashin waɗanda suka shiga zaɓe amma suka faɗi.

A jihar Katsina kuwa, an ga wani abin mamaki inda wata mace, Jamila, ta samu nasara a ƙaramar hukumar Mani da Bindawa da ƙuri’u 24,989, yayin da abokin takararta ya samu ƙuri’u 1,256.

Haka kuma a yankin Daura, Yusuf Buhari ya samu rinjaye da ƙuri’u 17,342, yayin da Auwalu Musa ya samu ƙuri’u 480 kamar yadda aka bayyana.

Dangane da jam’iyyun adawa kuwa, jaridar Leadership ta ranar 18/05/2026 ta ruwaito cewa jam’iyyar PRP ta bayyana cewa za a iya kayar da Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

To, a nan akwai tambaya: Shin manufar adawa kawai ita ce ƙwace mulki, ko kuwa neman sauyi da cigaban ƙasa da al’umma?

Shawarata ga talakawa ita ce kada siyasa ta zama sanadin yanke zumunci ko haddasa gaba a tsakanin jama’a. Kada mu bari a yi amfani da mu har mu zama gumakan yaƙi saboda siyasa.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Jihar Katsina. 07066434519/08080140820.

By ukarofi