
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APM a Jihar Bauchi, ta tabbatar da Dakta Yakubu Adamu da Hon. Mahmood Babamaji Abubakar a matsayin ‘yan takarar gwamna da mataimaki a zaɓen 2027 da ke tafe.
An bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin babban taron jam’iyyar da aka gudanar bayan kammala zaɓukan fidda gwani na APM a faɗin jihar.
Haka kuma, Gwamna Bala Abdulƙadir Mohammed na jihar ya fito a matsayin ɗan takarar sanatan Bauchi ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar.
Da yake jawabi bayan kammala taron, Dakta Yakubu Adamu ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta ɗora akan nasarorin da aka samu domin cigaban Jihar Bauchi,
Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su haɗa kai domin ganin sun cimma nasarori zaɓen 2027.
A nasa jawabin, Shugaban APM a Bauchi Auwal Isa, ya ce jam’iyyar ta shirya tsaf wajen ganin ta tunkari babban zaɓen 2027 yadda ya dace ta hanyar tsayar da ‘yan takarar da suka cancanta domin wakiltar ta a matakai daban-daban.
