
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sarkin Argungu, Muhammad Samaila-Mera ya kirayi al’ummar yankinsa da su mallaki makamai ta hanyar da doka ta tanada don ƙara karfin tsaro na gida da kuma kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
Haka kuma, ya buƙaci ƙauyukan da ke ƙarƙashin masarautarsa da kasancewa masu kula da sanya ido akan ayyukan ‘yan ta’adda da kan kai musu farmaki akai-akai, yana mai cewa ɗaukar matakin kare kai ta halastaccen hanya shi ne ya daci a matsayin lalura ga cigaba da taɓarɓarewar lamuran tsaro.
Sarkin ya bayyana haka ne a yau Jumma’a yayin wani taro tare da hakimai, dagatai, da masu unguwanni a fadarsa da ke Argungu.
Samaila-Mera ya jaddada buƙatar al’umma su ƙarfafa salon tattara bayanan sirri tare da gaggauta raba wa hukumomin tsaro bayannan da za su taimaka musu a ƙoƙarin magance matsalolin rashin tsaro da ke cigaba da addabar al’umma.
Kazalika, ya shawarci mazauna yankin da su haɗa kai wajen samar da albarkatu don siyan makamai da gwamnati ta amince da su don kariyar kai a dokance.
