Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jarrabawar ɗalibai masu kammala karatun sakandare ta WASSCE ta fuskanci tsaiko a cibiyoyi da dama a jihohin Kaduna, Katisna, Delta, Imo, Oyo, Legas, Ogun da Osun, inda aka tilasta musu rubutawa acikin duhu sakamakon jinkirin kawo kayayyakin jarrabawar a wuraren da aka ɗauke wutar lantarki.
Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin, wanda ya ɗauki tsawon kwanaki, ya jefa ɗalibai da dama cikin mawuyacin hali a cibiyoyin na sa’o’i, inda a wasu lokutan ake tilasta musu rubutawa a yanayin lantarki mara inganci.
Waɗansu rahotanni sun nuna cewa an fara fuskantar ƙalubalen ne tun a ranar Litinin, a lokacin da wasu ɗalibai ke rubuta jarrabawar Physics da aka sanya za a yi ta ƙarfe 2 da 3:30 na rana sakamakon jinkirin kawo takardun da ya jefa su a halin.
An ruwaito cewa, al’amarin ya cigaba da faruwa har zuwa ranar Laraba, inda aka fara jarrabawar darasin Lissafi ƙarfe 6:30 na yamma a wasu wuraren da kuma kusan ƙarfe 8:30 a wasu.
Wannan al’amari ya sa da dama daga cikin ɗaliban ba su samu damar kammalawa ba har sai 10 na dare, wanda ya haifar da damuwa acikin iyaye, masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da ma ɗaukacin al’umma.
An ce, al’amarin ya fi tsanani ne a wasu yankunan Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, inda ɗaliban suka samu jinkiri yayin fara rubuta jarrabawar gwaji ta darasin Kimiyyar Noma.
