Vinicius zai iya barin Real Madrid idan ya so – Perez

Spread the love

Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Florentino Perez, ya bayyana cewa ba zai hana tauraron ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Vinicius Junior, barin ƙungiyar ba idan har ya yanke shawarar komawa wata ƙungiya.

Kalaman na Perez sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan sabunta kwantiragin ɗan wasan na Brazil, tattaunawar da har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba.

Da yake magana kan raɗe-raɗin da ke yawo game da makomar Vinicius, shugaban na Real Madrid ya bayyana cewa yana da burin ganin ɗan wasan ya ci gaba da zama a ƙungiyar har ƙarshen rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.

A cewar rahoton jaridar El Pais, Perez ya ce Vinicius yana da alaƙa ta musamman da Real Madrid, kuma yana daga cikin fitattun ‘yan wasan da suka zama wani ɓangare na tarihin ƙungiyar.

Sai dai shugaban ya jaddada cewa ba zai tilasta wa ɗan wasan zama a ƙungiyar ba idan ya daina sha’awar ci gaba da taka leda a Santiago Bernabeu.

Perez ya ce, idan Vinicius ya ga ya kamata ya rattaba hannu da wata ƙungiya daban, to zai samu cikakken ‘yanci ya yi hakan ba tare da wani cikas daga mahukuntan Real Madrid ba.

Har ila yau, shugaban ya musanta zargin cewa batun albashi ne ya janyo tsaiko a tattaunawar sabunta kwantiragin.

Ya ce kuɗi ba su taɓa zama babban abin da ke jagorantar irin waɗannan tattaunawa ba, yana mai cewa akwai sauran lokaci kafin a yanke hukunci kan sabon yarjejeniya.

“Zan so Vinicius ya zauna tare da mu har ƙarshen rayuwarsa. Yana da alaƙa mai ƙarfi da wannan ƙungiya. Amma idan ya yanke shawarar barin Madrid domin wata ƙungiya, zai kasance da cikakken ‘yanci. Ba zan tilasta masa komai ba,” inji Perez.

Duk da wannan yanayi, Vinicius har yanzu yana da ragowar kwantiragi da Real Madrid har zuwa watan Yunin shekarar 2027.

Rahotanni daga kafofin yaɗa labarai daban-daban sun nuna cewa babban abin da ke kawo tsaiko shi ne bukatar karin albashi daga ɓangaren ɗan wasan, inda ake cewa masu kula da harkokinsa suna son a daidaita albashinsa da na manyan taurarin ƙungiyar ciki har da Kylian Mbappe.

A gefe guda kuma, Real Madrid na son ci gaba da bin tsarin albashin da take amfani da shi a cikin ƙungiyar, yayin da wasu manyan ƙungiyoyin gasar Firimiya ta Ingila da kuma ƙungiyoyin Saudi Arabia ke bibiyar lamarin da idon basira.

Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa Vinicius ya bai wa shugabannin Real Madrid tabbacin cewa ba zai bari kwantiraginsa ya ƙare ya tafi kyauta a shekarar 2027 ba.

Wannan na nufin idan har bangarorin biyu suka kasa cimma matsaya kan sabon kwantiragi, ƙungiyar za ta iya sayar da shi a wata babbar ciniki maimakon rasa shi ba tare da samun ko sisi ba.

By ukarofi