
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda ta ceto Mrs Olaide Busayo Adegoke John-Paul da ‘yan biyunta maza masu shekara 12, Peter da Paul a raye a wani atisaye da aka ƙaddamar da misalin ƙarfe 8:30 na dare a ranar Lahadi.
A cewar wata majiya daga rundunar da ta magantu akan al’amarin bisa sharaɗin sakaye sunansa, an halaka mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin da ƙwato wasu bindigogi guda biyu a yayin ceton.
Cikin waɗanda al’amarin ya shafa akwai ƙanwar tsohon Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, da aka sace su da misalin ƙarfe 7:30 na safe a ranar 3 ga Yuni, 2026, yayin da suke kan hanyar kai yaran makaranta a Ibadan, Jihar Oyo.
Majiyoyin ‘yan sanda sun ce aikin leƙen asiri na bin diddigi da matsin salon aiki ya taimaka wajen tilasta wa masu garkuwar yin fito-na-fito da jami’an, lamarin da ya taimaka wajen ceto su cikin ƙoshin lafiya.
Haka kuma, sun ce a yanzu haka jami’an tsaro na cigaba da farautar waɗanda suka tsere daga cikin ‘yan bindigar da suka samu raunukan harbi.
Bayan garkuwa da su, Gwamna Seyi Makinde na Jihar ya ziyarci Adelabu a ranar Juma’a, inda ya tabbatar masa da cewa ana ƙoƙarin ganin an ceto su cikin aminci.
An sace su ne makonni da yi awon-gaba da ɗalibai 40 da malamai a wasu makarantu da ke Ƙaramar Hukumar Oriire na jihar, lamarin da ya haddasa cece-kuce a sassan Nijeriya.
