Gamji Uban Fita Kunya!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kai tsaye a wannan kafa na kawo bayanan jami’i a gidan rediyon Biyafara Chinasa Nworu ya faɗi burinsu kan Arewa na wargaza yankin da maida shi ‘yan garuruwa ƙarƙashin mulkin ƙabilu. Nworu ya fito da hoton ‘yan karyar Hausa zalla da dama ba su da wata alaƙa da Hausawa ya jinjina mu su. Yanzu haka wasu daga gaggan ‘yan kwangilar karya ta Hausa zalla sun koma aiki kai tsaye da ‘yan IPOB kuma hakan ta tabbata a shafin Anyamuri Madu lion AJaja da ke Teɗas a Amurka. Tun watannin baya IPOB ke kashe dala 60,000 wato kimanin Naira miliyan 80 duk wata don samun karɓuwa a Amurka ta marawa Biyafara baya musamman a ƙarƙashin mulkin nan na Donald Trump. Idan har a Amurka kaɗai ga kamfanonin bin-kafa IPOB na kashe dala 60,000 sai ‘yan karyar Hausa zalla za su yi bayanin dala dubu na wa su ke samu.

Akwai kananan yara da ba mamaki bai fi na DATA a ke tura mu su, su kasa sayen indomie don maganin yunwa, su zuba kuɗi a waya su wuni su na zunduma ashar ta ba gaira ba dalili ga uban fita kunya Gamji Sir Ahmadu Bello wanda ya sadaukar da ransa don Arewa bai bar Fam ko Dala ba amma ya bar ayyukan Mahadi ka ture; ga dai jami’ar Ahmadu Bello. Yaro da bai dade da sauke shi a majanyi ba ga idanu kifil-kifil amma har zai iya zagin manyan malaman Musulunci da iyayen Arewa da ya dace addu’ar alheri a ke tsammani daga bakin kowa Musulmi da mabiya addinin Kirista. Kai matuƙar mutum ya san tarihin gaskiya na Sardauna wallahi sai ya zubar da hawaye don yadda ko barci mai nauyi ba ya iya yi don kula da amanar da Allah ya dora ma sa ta al’umma. Chief Sunday Awoniyi, Dokta Ishaya Audu, Mr.Micheal Audu Buba, Gwamna Awan na Kagoro, Danmasanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule duk shaidu ne na tsantsar amanar Sardauna.

Miyagun iri su Chukwuma Nzeogwu su ka saka bindiga a 1966 su ka shekar da jinin Gamji amma an haifi yaro a 1995 ko 2005 sai wasu su ma sa mummunar tarbiyya ya hau soshiyal midiya ya na aibata mutanen da bai san girman darajarsu ba sam! Shi ma bai san ma inda duniya ta dosa ba amma macizai sun cusa ma sa tatsuniyoyin ƙiyayya ba ya ganin girman na gaba da shi.

’Yan karyar Hausa zalla da yaudarar IPOB ta Arewa wato IPOH ku fito ka faɗa mana dala nawa IPoB ke ba ku duk wata kan kwangilar zagin Gamji da Mujaddadi. Tabbas ku rubuta ku ajiye duk sharrinku ba yadda za a yi makiya Sardauna da Mujaddadi Shehu Usamnu Danfodio su mulki Arewa.

Yo wani na tunanin akwai ɓatanci da zai sa a manta da ta’addancin Chukwuma Nzeogwu don dora ‘yan IPOB a fadar Aso Rock su sako na gidan yarin Sakkwato don cigaba da ingiza mayakansa su na kisan gilla? ha sama ta yi wa yaro nisa sai dai ya sa ido ya yi kallo. Jostis James Omotosho na babbar kotun tarayya ya gama yanke hukunci kuma ya yi sassauci ma don sai da ya ɗauko karatu daga BIBLE na kare darajar rai kafin hukuncin da asalin laifin cin amanar ƙasa mafi girman hukunci ya ke ƙunshe da shi wato hukuncin kisa.

Duk fitinar Arewa kama daga ɓarayin daji zuwa safarar miyagun ƙwayoyi da shigo da jabun kaya har da ɗaukar nauyin kwangilar zallawa duk aikin miyagun nan ne don sun rasa yadda za su yi da Arewa su rage ma ta tasiri a siyasance da a addinance. Kai kul akwai mamaki wani ɗan sullutun yaro ko wani mai makirci ya yi kasassabar cin zarafin gwamnatin Lardin Arewa bisa jagorancin Gamji.

Ni fa zuciyata na tabbatar min duk wanda ya shigo nan Arewa ya na aibata Sir Ahmadu Bello Sardauna to ba zai yi albarka ba kuma ba zai samu biyan buƙata ba. Marigayi Alhaji Musa Dankwairo ya duba ɓangaren bunƙasa ilimi kaɗai ma ya jinjinawa Gamji da zama NAMIJI UBAN ’YAN BOKO. Mu ma ai mun tabbatar da hakan don in ka yi misali da gagarumar jami’ar ABU da Sardauna ya assasa don dukkan al’ummar Arewa su amfana da ilimi mai zurfi ya kai wannan yabo har da kari. Duk wanda zai yi wani abu daga baya to albarkar su Gamji ya ke ci.

Biyo bayan wata sabuwar ajanda ta zubar da kyakkawan tarihin Gamji da ya danganci burin ‘yan siyasa na yau, kuma ya ci karo da kwangilar makiya Arewa da musulunci, na ji daɗi ainun da na ga ’yan bokon Arewa musamman matasa sun shigo da bayanai na tarihi mai sahihanci da ke fito da ɗimbin alheran Gamji. A baya duk hayaniyar da ‘yan bazata ke yi, ‘yan bokon nan sun yi shiru ba su tanka ba wanda ba mamaki don su na ɗaukar masu yin a iya soshiyal midiya su ke cin karensu ba babbaka. Yau ga rubuce-rubuce masu muhimmanci sun cike shafukan soshiyal midiya na Arewa da ke fito da sadaukar da kai na Gamji har ‘yan shan jini mugayen iri su ka yi ma sa kisan gilla a Kaduna ranar 1 ga watan Janairu 1966.

Haƙiƙa tun da ’yan boko na Arewa su ka shigo batun nan, sai hankula su ka dawo kan gaskiya da gane masu tada husuma da ke fakewa da ƙalubalen tsaro na Arewa maso yamma da ta tsakiya don zuga musulmi su hau ɗauki da daɗi da juna a doron ƙabilanci. In ba don wayar da masu tasowa da kuma waɗanda ba su da sahihin tarihi ba, tankawa masu ruruta wannan fitina ba shi da wani amfani don mutanen ma akasari da sunayen karya su ke aiki kuma ba lallai ma ‘yan Arewa ba ne in kuma ‘yan Arewa ne za ka taras kiyayya ce kawai ta bambancin addini da su Sardauna su ka ɗau matakan adalci da ya hana tasirin hakan a zamaninsu.

Zan so a samu wani haziƙin marubuci ya tattara irin waɗannan rubuce-rubuce na wayarwa a kundi daya a wallafa shi ko a littafi daya ko a wasu shafukan yanar gizo don zama abun zama madogara wajen sahihin tarihi ga ‘yan Arewa da za su taso nan gaba. Na ga marubuta irin su Ibrahim Sheme, Bashir Yahuza Malumfashi, Fatuhu Mustapha da sauran su, sun yi muhimmin rubutu na tarihi kan wannan darasi. Na ga matasa irin Muhammad I. Alkhizami na fito da bayanai da martani mai ma’ana don ankarar da jama’a tace gaskiya.

Ina kira ga duk masu kishin Arewa su cigaba da fitar da bayanai na ture makircin da a ke kullawa yankin don neman ganin bayansa. Aƙalla dai mu samu dama da yardar Allah mu bar wa na baya kyakkyawan tarihi kamar yadda mu ka amfana tun mu na makarantun firamare da ma sakandare da mu ka yi kararu kyauta da albarkacin ginshiƙin adalci da Sardauna da ‘yan majalisarsa su ka kafa. Alheri gadon barci yau ga shi akasarin ‘yan majalisar Gamji da na kusa da shi ba sa doron duniyar nan amma ayyukan na gina kasa na nan daram.

Idan mahaukacin kare ya yi haushi ba lallai sai an ɗau dutse an jefe shi don gudun kar ya kawo farmaki ba, hanyoyin dabaru na iya kwantar da ƙurarsa kuma a nan ina nufin a riƙa ture ƙarairayi da jahilci ta hanyar gaskiya da ilimi.

Mun san yadda ‘yan karyar Hausa zalla su ka zayyana Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da yarfe na ƙabilanci wajen mara baya ga ‘yan takara har ma da nuna wai shi Bafulatani ne zalla. Shin ma in an cire irin su Kwankwaso a Kano daga zama Hausawa waye Bahaushen ne? ‘yan karyar Hausa zalla da ke da tsamin baki na gwaranci in su na magana ko rubutu da Hausa ko ‘yan IPOB masu ɗaukar nauyin shigar burtun?. Yaudara da annamimanci miyagun ɗabi’u kuma duk daren daɗewa sai asirin masu yin haka ya tonusu girbi makircinsu tun a nan doron kasa.

Wallahi na ga inda zallawa su ka yi ta caccakar Kwankwaso da rubuta miyagun kalamai a kansa har ma da nuna kamar ba ma mai matsala irinsa amma tun da yanzu sun haɗa tafiya da Obi sai matsayar kwangilar ɓatancin ya fara sauyawa inda a yanzu farafagandar ta koma neman zubar da mutuncin iyayen siyasar Arewa da a ka yi wa kisan gilla.

Wani mutum daya ne ma mai tsananin ƙirƙirar sharri ya caccaki Madugu wai ya hana Malam Nasiru Gawuna tikitin takarar gwamna a NDC don haka wai ya tsani ‘yan zallawa. Ba inda na taɓa jin Gawuna ya zargi wani da ƙabilanci kuma shin a 2023 Bafulatani Dokta Abdullahi Umar Ganduje bai tsayar da Gawuna takarar gwamna ba? Kai mutanen nan tarkace ne masu tufka da warwara.

KAMMALAWA

Yayin da zallawa su ka zama hawainiya kan Dokta Kwankwaso, sun takarkare ga kwangilar ɓatanci ga Sir Ahmadu Bello don samawa ‘yan uwansu IPOB goyon baya a Arewa. Wallahi duk wanda ya zagi Gamji ya cancanci korar kare daga Arewa.

Kanawan gaskiya ba ‘yan shigar burtu ba ne, ba ruwansu da ƙabilanci ko wannan muguwar farafaganda da bakin haure ‘yan banza 7 makiya Hausawa, makiya Musulunci da Arewa ke yayatawa a soshiyal midiya.

By ukarofi

Leave a Reply