A cikin ’yan watannin nan, muhawara ta sake ɗaukar zafi a fagen siyasar Nijeriya kan yiwuwar ƙasar ta koma ƙarƙashin tsarin da jam’iyya guda ɗaya ke mamaye siyasa. Wannan muhawara ta samo asali ne sakamakon yawaitar sauya sheƙa da wasu manyan ’yan siyasa ke yi daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar da ke mulki, lamarin da ya sa wasu masu sharhi ke gargaɗin cewa dimokuraɗiyyar Nijeriya na iya fuskantar barazana idan ba a samu ƙarfi da daidaito tsakanin jam’iyyun siyasa ba.
Sai dai tambayar da ake yi ita ce: Shin da gaske Nijeriya na daf da zama ƙasar jam’iyya ɗaya? Kuma ko hakan ma zai yiwu a tsarin siyasar da Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ya tanada?
Mene ne tsarin jam’iyya ɗaya?
Tsarin jam’iyya ɗaya na nufin yanayin da jam’iyya guda ke da cikakken iko a harkokin siyasa, ta yadda sauran jam’iyyun ko dai ba sa da tasiri ko kuma an taƙaita musu damar fafatawa.
A wasu ƙasashe irin su Chana, Cuba da Koriya ta Arewa, dokoki ne ke ba jam’iyya guda damar mulki. Amma a wasu ƙasashe kuwa, ko da yake akwai jam’iyyu da dama a rubuce, jam’iyya guda ce ke ci gaba da lashe zaɓe saboda ƙarfin da take da shi a siyasa da tattalin arziki.
Masana kimiyyar siyasa suna bayyana cewa akwai bambanci tsakanin ƙasar da ke da jam’iyya guda a hukumance da kuma ƙasar da jam’iyya guda ke mamaye siyasa sakamakon raunanan jam’iyyun adawa.
Tarihin siyasar Nijeriya:
Tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, Nijeriya ta kasance ƙasa mai jam’iyyu da dama. A farkon Jamhuriya ta Huɗu, Jam’iyyar PDP ta mamaye siyasa tsawon shekaru 16, daga 1999 zuwa 2015.
A lokacin, PDP ta mallaki mafi yawan jihohi, kujerun majalisu da kuma shugabancin ƙasa. Har ma wani lokaci wasu jiga-jiganta sun bayyana cewa za ta mulki Nijeriya na shekaru 60.
Sai dai a shekarar 2015, haɗakar jam’iyyun adawa ta haifar da kafuwar APC, wadda ta kayar da PDP a zaɓen shugaban ƙasa. Wannan ya nuna cewa duk wata jam’iyya da ta yi ƙarfi a Nijeriya za ta iya fuskantar ƙalubale idan adawa ta haɗu.
Dalilan da ke haifar da fargabar jam’iyya ɗaya:
A halin yanzu akwai wasu abubuwa da ke ƙara janyo wannan muhawara.
Na farko shi ne yawaitar sauya sheƙar gwamnoni, ‘yan majalisu da wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa APC.
Na biyu shi ne rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye manyan jam’iyyun adawa, musamman PDP, ADC da LP, wanda ya rage musu ƙarfin yin hamayya.
Na uku kuma shi ne yadda jam’iyyar APC ke ci gaba da riƙe iko a matakin tarayya tare da samun rinjaye a jihohi da dama.
Waɗannan abubuwa sun sa wasu ‘yan siyasa da masu rajin dimokuraɗiyya ke nuna damuwa cewa idan aka ci gaba da wannan yanayi, za a iya samun gagarumin rashin daidaito a siyasar ƙasar.
Shin Kundin Tsarin Mulki ya amince da hakan?
Masana harkokin shari’a sun bayyana cewa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya bai ba da damar kafa tsarin jam’iyya guda ɗaya ba.
Sashe na 40 na kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa ‘yan ƙasa damar kafa ƙungiyoyi da jam’iyyun siyasa. Haka kuma, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) na da alhakin rajista da kula da jam’iyyun siyasa.
Saboda haka, babu wata hanya ta doka da za a iya hana jam’iyyun adawa wanzuwa muddin suna bin dokokin ƙasa.
Sai dai masana suna gargaɗin cewa ko da kundin tsarin mulki ya amince da jam’iyyu da dama, idan jam’iyyun adawa suka raunana ƙwarai, hakan na iya haifar da yanayin da jam’iyya guda za ta mamaye siyasa a aikace.
Abubuwan da ka iya hana faruwar hakan:
Akwai dalilai masu yawa da ke nuna cewa ba abu ne mai sauƙi Nijeriya ta koma ƙasar jam’iyya ɗaya ba.
1. Yanayin bambance-bambancen Nijeriya
Nijeriya ƙasa ce mai yawan ƙabilu, addinai da yankuna. Wannan bambancin ya sa siyasa ke da matuƙar rikitarwa.
Jam’iyyar da ta yi ƙarfi a wani yanki na iya rasa karɓuwa a wani yanki. Wannan yanayi na taimakawa wajen tabbatar da cewa babu wata jam’iyya da za ta iya mamaye ƙasar gaba ɗaya cikin sauƙi.
2. Tarihin sauyin siyasa
Tarihin siyasar Nijeriya ya nuna cewa babu wata jam’iyya da ke da tabbacin mulki har abada.
PDP ta yi mulki tsawon shekaru 16 amma daga ƙarshe ta rasa iko. Wannan ya nuna cewa ko APC ma za ta iya fuskantar irin wannan ƙalubale idan ta rasa goyon bayan jama’a.
3. Tasirin kafofin sadarwa da ƙungiyoyin fararen hula
A yau, kafafen sada zumunta da ƙungiyoyin fararen hula sun zama masu tasiri wajen sa ido kan gwamnati da kare dimokuraɗiyya.
Wannan ya sa duk wani yunƙuri na tauye tsarin dimokuraɗiyya ke fuskantar ƙalubale daga jama’a.
4. Matsayin hukumar zaɓe
Duk da cewa ana yawan sukar tsarin zaɓe, kasancewar akwai Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa na taimakawa wajen tabbatar da cewa jam’iyyu daban-daban suna da damar shiga zaɓe.
Me masana ke cewa?
Wasu masana kimiyyar siyasa suna ganin cewa abin da ake gani a yanzu ba yunƙurin kafa jam’iyya guda ba ne, illa raunin jam’iyyun adawa.
A cewarsu, idan jam’iyyun adawa suka warware matsalolinsu na cikin gida, suka gabatar da manufofi masu gamsarwa tare da haɗin kai, za su iya sake zama barazana ga jam’iyyar da ke mulki.
Sai dai wasu na ganin cewa idan aka ci gaba da sauya sheƙa ba tare da tsari ba, za a iya samun yanayin da zaɓe zai rasa armashin gasa, wanda hakan zai iya cutar da dimokuraɗiyya.
Darasin da ake iya koya:
Tarihin dimokuraɗiyya a duniya ya nuna cewa ƙarfi da ɗorewar tsarin siyasa na dogara ne kan kasancewar adawa mai ƙarfi.
Lokacin da babu adawa mai tasiri, gwamnati kan rasa matsin lambar da ke sa ta yi aiki yadda ya kamata. Hakan na iya haifar da almundahana, rashin gaskiya da kuma gazawar shugabanci.
Saboda haka, ko jam’iyyar da ke mulki ko jam’iyyun adawa, duk suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da cewa dimokurɗiyyar Nijeriya ta ci gaba da ƙarfi.
Duk da fargabar da ake nunawa game da yiwuwar Nijeriya ta koma ƙarƙashin tsarin jam’iyya ɗaya, masana da dama suna ganin hakan ba abu ne mai sauƙi ba a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma yanayin siyasar Nijeriya.
Abin da ya fi bayyana a yanzu shi ne raunin wasu jam’iyyun adawa da kuma ƙarfin jam’iyyar da ke mulki. Amma tarihin siyasar Nijeriya ya nuna cewa iko na sauyawa, kuma babu wata jam’iyya da za ta iya ɗaukar kanta a matsayin mai mulkin har abada.
Makomar siyasar Nijeriya za ta ta’allaƙa ne kan yadda jam’iyyun siyasa, hukumomin dimokuraɗiyya da kuma al’umma za su ci gaba da kare tsarin da ya bai wa kowa damar shiga takara da neman amincewar jama’a.
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. 07066778190.
