Daga MUSA AHMAD
Ƙorafin tsare yarinya ta hanyar nuna ɓangaranci sa shirin jefa alƙalin hisba cikin tsaka mai wuya
KANO – Zarge-zargen rashin adalci da nuna son rai sun mamaye al’umma bayan ɓullar ƙorafe-ƙorafen da ke alaƙanta wani alƙalin hukumar Hisba, Sani Tanimu, da abin da masu ƙorafi suka bayyana a matsayin tauye haƙƙin wata yarinya marar gata.
Lamarin ya janyo cece-kuce, inda jama’a ke kira ga mahukunta su gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.
Rahotanni sun nuna cewa tunda farko rikici ne ya ɓarke tsakanin wasu mata biyu, lamarin da ya kai ga shigar da maganar hannun jami’an tsaro. Sai dai duk da cewa ɓangarorin da abin ya shafa sun nuna alamun sasantawa, saidai wani mutum mai ƙumbar susa ya daddage sai an ci gaba da shari’ar tare da ɗaukar matakan da suka fi tsauri kan ɗaya daga cikin ɓangarorin.
Jaridar Alfijir Labarai ta rawaito cewar masu ƙorafin sun yi zargin cewa wani tsohon alƙali mai suna Idris Yahya, wanda aka fi sani da “Mai Hannu Ɗaya”, ya taka rawa wajen yadda aka tafiyar da shari’ar. Sun ce tun kafin a gurfanar da yarinyar a gaban kotu an riga an tsara yadda za a tabbatar an tsare ta, lamarin da ya sa ake zargin cewa an yi amfani da dangantaka da kusanci wajen karkatar da akalar adalci.
A cewar bayanan da suka fito daga iyalan yarinyar, an kai ta gidan gyaran hali tun bayan gurfanar da ita a kotun Hisba duk da ƙarancin shekarunta. An ce duk ƙoƙarin da aka yi na neman a ba ita beli, amma lamarin ya gagari kundila, yayin da alƙalin ya ci gaba da ƙin amincewa da buƙatar, abin da ya ƙara jefa iyalanta cikin damuwa da tashin hankali.
Bayan dawowar kotu daga hutun ƙarshen mako, an sake mayar da yarinyar gidan gyaran hali, inda ta ƙara kwashe wasu kwanaki a tsare kafin daga bisani aka samu damar fitar da ita da beli. Wannan mataki ne ya ƙara fusata iyalanta, waɗanda ke ganin cewa an nuna wariya da tsanani fiye da yadda yanayin rikicin ya kamata ya haifar.
Masu bibiyar harkokin shari’a sun bayyana cewa idan har waɗannan zarge-zarge suka tabbata, to lamarin na nuna wani mummunan yanayi da ke iya rusa amincewar jama’a ga tsarin adalci. Sun ce babu abin da ya fi cutar da al’umma kamar ganin cewa mai ƙarfi na iya rinjayar hukunci yayin da marar gata ke zama wanda ake danniya a kansa.
Har ila yau, wasu na ganin cewa wannan batu ya wuce rikicin mata kawai, domin ya shafi mutuncin hukumomin da aka ɗorawa alhakin kare hakkokin jama’a. A cewarsu, duk lokacin da aka samu zargin cewa ana haɗa baki da masu faɗa a ji wajen muzanta talaka, wajibi ne hukumomi su fito su tabbatar da gaskiya domin kawar da duk wata shakka.
Masu sharhi kan lamuran shari’a sun buƙaci Gwamnan Jihar Kano da mahukuntan ɓangaren shari’a da su buɗe cikakken bincike kan lamarin. Domin jama’a na son a gano ko an bi ƙa’idojin doka yadda ya kamata ko kuma akwai wasu hannaye da suka yi tasiri wajen tsawaita tsare yarinyar fiye da yadda doka da adalci suka tanada.
Masu ƙorafin sun jaddada cewa idan gwamnati ta yi shiru a kan irin wannan zargi, hakan zai ƙara ƙarfafa tunanin cewa talaka ba shi da gata a gaban wasu masu iko. Sun ce lokaci ya yi da za a tabbatar wa al’umma cewa adalci ba na masu kuɗi da masu faɗa a ji kaɗai ba ne, kuma duk wanda aka samu da laifin karkatar da gaskiya ko amfani da matsayinsa wajen zaluntar marasa ƙarfi dole ne ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
Ahmad ya rubuto ne daga Kano
