Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai sake neman wa’adin mulki a zaɓen da ake sa ran gudanarwa a bana, kamar yadda jam’iyyarsa ta Likud ta tabbatar a ranar Laraba, bayan wasu kalamai daga Shugaban Amurka Donald Trump sun haifar da tambayoyi kan ko zai sake shiga takara ko kuwa.
A cikin takaitaccen sanarwar da jam’iyyar Likud ta fitar, ta bayyana cewa Netanyahu zai tsaya takara a zaɓen, tare da nuna fatan cewa, da yardar Allah, zai sake samun nasara.
Ko da yake har yanzu ba a ayyana ranar gudanar da zaɓen a hukumance ba, dokokin ƙasar sun tanadi cewa dole ne a gudanar da shi kafin watan Oktoba na wannan shekara.
Tun da farko dai babban wakilin ABC News da ke Washington, Jonathan Karl, ya wallafa a shafinsa na ɗ cewa Donald Trump ya shaida masa bai tabbatar ko Netanyahu zai sake tsayawa takara ba.
A cewar Karl, Trump ya ce, “Ban sani ba. Ya yi wata gagarumar tafiya a siyasa. Tambayar ita ce, shin har yanzu yana son ci gaba?”
Wannan zabe mai zuwa zai kasance na farko tun bayan harin da ƙungiyar Hamas ta kai ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda aka bayyana a matsayin daya daga cikin manyan gazawar tsaro mafi muni a tarihin Isra’ila, kuma wanda daga bisani ya haifar da yakin da Isra’ila ta kaddamar a Zirin Gaza.
Netanyahu ya dawo mulki ne a watan Disamban 2022 a matsayin jagoran gwamnatin hadaka mafi tsattsauran ra’ayi a tarihin siyasar Isra’ila. Tun daga lokacin yake fuskantar ƙalubale masu yawa, ciki har da zanga-zangar kin gwamnati da kuma rikice-rikicen yaki a Gaza, Lebanon da Iran.
Duk da ci gaba da rike madafun iko, kuri’un jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a lokuta daban-daban sun nuna cewa kawancen jam’iyyarsa na iya kasa samun rinjayen kujerun majalisa idan aka gudanar da zabe a yanzu.
Wani sabon bincike da cibiyar nazarin dimokuradiyya ta Israel Democracy Institute ta fitar a ranar 9 ga Yuni ya nuna cewa kashi 61 cikin 100 na ‘yan Isra’ila na ganin bai kamata Netanyahu ya sake tsayawa takara ba.
Sai dai kuma wasu kuri’un sun nuna cewa jam’iyyun adawa ma ba za su iya samun cikakken rinjaye a majalisa ba sai idan sun hada kai da jam’iyyun Larabawa, matakin da wasu daga cikin shugabannin adawar suka bayyana cewa ba su shirya dauka ba.
A gefe guda kuma, jami’an Amurka da na Isra’ila sun bayyana cewa duk da wasu lokutan sabani, har yanzu dangantaka tsakanin Donald Trump da Benjamin Netanyahu na nan daram.
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin biyu sun hada kai wajen fara yakin Iran a watan Fabrairu, ko da yake an samu wasu matsaloli a baya-bayan nan yayin da Trump ke matsa wa Isra’ila ta rage kai hare-haren soja a Lebanon domin bai wa tattaunawar sulhu da ake yi tsakanin Washington da Tehran damar samun nasara.
A makon da ya gabata ma Trump ya amince cewa a cikin wata tattaunawa mai zafi ta wayar tarho ya taba kiran Netanyahu da kalmar batanci mai tsauri, amma duk da haka ya ce har yanzu suna da kyakkyawar alaka.
Baya ga haka, Trump ya sha yin kira ga shugaban Isra’ila da ya yi afuwa ga Netanyahu kan tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa da ake yi masa a kotu, zarge-zargen da firaministan ke ci gaba da musantawa tare da dagewa cewa ba su da tushe.
