Akalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon sabbin hare-haren sama da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon a ranar Laraba, kamar yadda majiyoyin tsaro na Lebanon suka bayyana, a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da matsa kaimi wajen kai farmaki kan kungiyar Hezbollah, yayin da ita kuma ƙungiyar mai samun goyon bayan Iran ke iƙirarin kai sabbin hare-hare kan dakarun Isra’ila a kudancin ƙasar.
Rahotannin cikin gida sun nuna cewa cikin waɗanda suka mutu akwai mutum tara da suka rasa rayukansu a ƙauyen Dayr Debba, mai nisan kusan kilomita takwas daga gabashin birnin Tyre.
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Lebanon ya tabbatar da wannan rahoto, yayin da hotunan bidiyo da Reuters ta samu suka nuna motoci na ci da wuta a birnin Sidon da ke kudancin ƙasar bayan wani hari ta sama da Isra’ila ta kai.
Fiye da watanni uku ke nan da harin haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran ya haddasa sabon babin rikicin da ya bazu zuwa sassa daban-daban na Gabas ta Tsakiya, inda Lebanon ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan filayen wannan yaki.
Rikicin ya ƙara ɗaukar sabon salo a farkon wannan makon bayan da Isra’ila ta kai hari kan unguwannin kudancin Beirut da Hezbollah ke da ƙarfi a cikinsu.
Wannan mataki ya janyo Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila, lamarin da ya sa Isra’ila ta sake kai farmaki cikin Iran kafin daga bisani ɓangarorin biyu su dakatar da musayar hare-haren.
Bisa kididdigar Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon, tun daga ranar 2 ga watan Maris hare-haren Isra’ila sun yi sanadin mutuwar kusan mutum 3,700 a ƙasar, ciki har da mata da yara da jami’an kiwon lafiya 730.
Hakazalika hukumomin ƙasar sun bayyana cewa kimanin mutum miliyan 1.2 sun rasa matsugunansu sakamakon ci gaba da yaki da hare-haren da ake kaiwa a yankuna daban-daban.
A nata bangaren, kungiyar Hezbollah ta sanar da shiga wannan rikici ne tun ranar 2 ga watan Maris, inda ta bayyana cewa matakin nata martani ne ga kisan Jagoran Addini na Iran da aka kashe a farkon ɓarkewar rikicin.
Tun daga lokacin, alkaluman da aka tattara daga sanarwar rundunar sojin Isra’ila sun nuna cewa akalla sojojin Isra’ila 28 sun mutu a fafatawar da ake yi a Lebanon, yayin da hare-haren Hezbollah suka kashe fararen hula hudu a ɓangaren Isra’ila.
A wani sabon ci gaba kuma, rundunar sojin Lebanon ta sanar da cewa wani jami’inta ya rasu a ranar Laraba sakamakon raunukan da ya samu a wani harin sama na Isra’ila da aka kai a kudancin ƙasar tun ranar 17 ga watan Maris, lamarin da ke ƙara nuna irin girman asarar rayuka da wannan rikici ke haddasawa a kullum.
