Sabon makamin Iran

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Iran ta samo wani sabon makami wanda daga dukkan alamu ya fi makamanta masu linzami da cikin Donald Trump da shugabannin kasashen yankin Gulf durar ruwa.

Ba kawai matsin tattalin arziki da ya fara addabar Amurka ba, ko barazanar dosar zaben Yan majalisa na Amurka, ko ma tsabar hasarar da Amurka ta yi na daruruwan biliyoyin daloli a gabas ta tsakiya sakamakon yakin kwana 39 ba, akwai bayanai da Amurka ta samu wanda ya girgiza ta, ta ke kokarin ganin ba ta ci gaba da yakin nan ba.

Iran ta gano sabon makaminta wanda barazanar amfani da shi kadai tabisa saka duk wani Mai hankali ya yi taka tsantsan. Zirin kogin Hormuz, wanda a yanzu haka ke karkashin ikon sojojin Iran, yanki da ke dauke da ilahirin numfashin gabas ta tsakiya a kan harkokin sadarwar zamani ta internet. A tsakanin wannan Dan tsukuku na fadin kilomita 40, akwai kimanin wayoyin cable (fibre optic cables) da ke dauke da internet guda bakwai da su ka hada kasashen Gulf gaba dayansu da kasashen Asiya, Afirka da Turai.

Akwai wayar AAE1 (Asia-Africa-Europe) mai tsawon kilomita 25,000 da ta hada wadannan nahiyoyin. Sannan akwai wayar FALCON wadda ke da tsawon kilomita 11,000 da ta hada India, Maldives, Egypt da kasashen Gulf. Akwai Kuma GBI (Gulf Bridge International) wadda ta hada kasashen Gulf, Italy da India Mai tsawon kilomita 5270. Sai ta karshe wadda ke da tsawon kilomita 380 da ta hada Kuwait da Iran.

Waɗannan wayoyin sun fara ne a tudu a kasashen yankin Gulf. Misali na AAE1 da FALCON daga garin Fujaira a UAE. Akwai wanda ya fara da ga garin Muscat a Oman. Sannan akwai na Bandar Abas da ke kasar Iran da kuma na GBI wanda ya faro daga garuruwa Doha (Qatar) da Manama (Bahrain). Kasancewar wurin a tsuke ya ke, kuma makogwaron (choke point) daga garin Musandam na Oman zuwa gabar ruwan Iran duk bai fi fadin kilomita 40 ba, ko bisa kuskure aka lalata guda zai iya shafar sauran, abinda zai kawo babbar matsalar sadarwa a nahiyoyin Asia, Afirka, Turai da yankin Gulf.

Sakamakon Iran na da kananan jirage masu dogon nutso a karkashin ruwa kuma bayanan sirri na nuna cewa a ziyara Arragchi Moscow a watan da ya gabata ya sami sirrin taswirar duk wadannan wayoyin na karkashin teku, Iran na shirin kai musu farmaki su lalata su matukar Amurka ta kai mata hari lokacin da a makon da ya gabata Donald Trump ya gama shiri tsaf na kai harin. Awanni biyu kafin ya bada odar harin masana a Amurka su ka bashi labarin wannan shiri na Iran. Dalilin da ya sa katsam aka ga yayi sanarwar dakatar da harin.

Wannan dalilin ya matukar harzuka Israila, dalilin da su ka zafafa kai hare-hare kasar Lebanon da kuma barazanar Kai hari Beirut. Wannan barazana da kuma aiwatar da ita a jiya ya sa Iran, kamar yadda ta yi gargadin dawo da kaiwa Israila hari matukar ta taba Beirut. Kuma Israila na kai wannan hari Iran ta cika alkawarin ta na dawo da hare hare kan Israila.

Donald Trump ya gargadi Israila da kada ta rama harin Iran saboda ya san matukar yakin ya ci gaba, kuma idan Amurka ta sake shiga, babu makawa Iran za ta yi amfani da wannan sabon makami nata mara linzami wanda zai durkusar da tattalin arziki da hada-hadar internet a Duniya gabaɗaya.

Kifi na kallon ka mai jar koma!!!

Ali manazarci ne a Kano

By ukarofi

Leave a Reply