Hajjin 2026: Alhazai 4,256 na Jihar Kebbi sun dawo gida

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi

Dukkan alhazai 4,256 daga Jihar Kebbi da su kayi aikin hajjin bana sun dawo gida lafiya, ba tared a wani ya rasu ba.

Haka kuma, hukumar jin daɗin alhazai ta jihar ta kwaso jakunkuna 7,860 na alhazai daga ƙasa mai tsarki zuwa Birnin Kebbi, kuma an miƙa su ga masu su.

Shugaban zartaswa na hukumar, Faruk Aliyu Yaro Enabo ya bada ƙididdigar a Birnin Kebbi, ranar Asabar sa’ilin taron kammala aikacen-aikacen aikin hajjin 2026.

“Nasarar da muka samu na aikin hajjin bana, sanadiyyar irin goyon baya da bada dukan kayayyakin aiki da Gwamna Nasir Idris ya yi ma hukumar ne domin ta samu nasara”

“An fayyace cewar Jihar Kebbi ce tafi sauran duk jihohin Najeriya shirye-shirye mafi inganci, tun daga nan gida har zuwa ƙasar Saudiyya”,

“Wani Alhaji tilo ne, yake shan magani a Makkah, kuma yana kan hanyarsa zuwa dawowa gida; muna ƙara godiya ga Allah, cewar babu wani Alhaji, namiji ko mace na Jihar Kebbi da ya rasu, dukanmu mun dawo gida cikin ƙoshin lafiya”, Enabo ya ce.

Shugaban hukumar ya shaida ma taron cewar, ƙa’idojin aikin hajjin 2027, sun fi na bana tsauri.

“Hukumomin Saudiyya sun bai wa maniyyatan aikin hajjin 2027 na duk duniya, wa’adin wata biyar na samun takardar iznin shiga ƙasa daga yanzu zuwa 1 ga watan Disamba, 2026”,

“Maniyyata daga Jihar Kebbi an umurcesu da su fara biyan kuɗin aikin Hajji na 2027 daga yau, kuma za’a kulle biya a ranar 30 ga watan Yuli, 2026”,

“Gwamna Nasir Idris ya yarda cewar maniyyata na iya fara ajiye kuɗin kujera Naira miliyan biyar, amma waɗanda ke da hali, suna iya biyan kudin kujera gaba daya, Naira miliyan bakwai”, Enabo ya yi bayani.

A lokacin taron, hukumar jin daɗin Alhazai, ta bai wa hukumomin tsaro kyauta da ya ƙunshi kuɗaɗe, da kuma sauran wasu mutane da suka bada gudunmawar da ta cancanta wurin samun nasarar aikin Hajjin 2026.

Hukumomin sune, shiga-da-fice da ‘yan sanda, Sojoji, DSS da Civil Defence da NAPTIP, da hukumar hana fasa ƙwabri, da hukumar kare haɗura.

Sauran sun haɗa, da kwamitin kiwon lafiya da ‘yan jarida da KTA, a yayin da wasu mutane guda huɗu aka bai wa kowanensu babur sabo-kar, saboda ƙwazon da su kayi wurin gudanar da ayyukansu.

Shugaban ayarin gwamnati kuma Amirul Hajj, Kwantirola-Janar mai murabus, na gidajen yari, Ahmad Jafar Jega, da Sarkin Kabin Jega, Muhammad Bawa Arzika, da kuma sauran wakilan kwamitin, sun halarci taron na kawo ƙarshen aikin hajji na shekarar 2026.

By ukarofi

Leave a Reply