Kotu ta saurari saƙon muryar Sirika kan kwangilar Air Nigeria

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

An samu sabon sauyi a shari’ar zargin damfara da ta shafi kwangilar harkokin sufurin jiragen sama ta Naira biliyan 2.8 da ake yi wa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, bayan da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar da wani saƙon murya da ake zargin nasa ne a gaban Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya dake Maitama a Abuja.

An kunna saƙon muryar ne a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji a zaman kotun na ranar Laraba, bayan da matsalolin fasaha suka hana sauraron sa a zaman da ya gabata.

Shaida ta 12 a ɓangaren masu gabatar da ƙara, Christopher Odofin, ne ya tabbatar da saƙon muryar a matsayin hujja, yayin da lauyoyin masu kare Sirika ba su musanta cewa muryar ba ta Sirika ba ce.

EFCC ta ce, tsohon ministan yana fuskantar tuhume-tuhume guda shida da suka shafi zargin cin hanci da rashawa dangane da wata kwangilar harkokin jiragen sama ta Naira biliyan 2.8. A zaman kotun, masu gabatar da ƙara sun miƙa faifan murya na CD ɗin da ke ɗauke da saƙon muryar a matsayin hujja, domin kotu ta saurari abin da ke cikinsa.

Bayan sauraron saƙon, lauyoyin Sirika da na kamfanin da ake tuhuma tare da shi, Michael Numa da Sanusi Mohammed, sun ce za su gabatar da ƙalubalensu kan amincewa da hujjar a lokacin gabatar da rubutattun hujjojinsu na ƙarshe.

A cikin saƙon muryar da aka kunna a kotu, an ji Sirika yana umartar tsohon Sakatare na Dindindin a Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama, Abel Enitan, da ya sauƙaƙa bayar da wata kwangilar ba da shawara ga wani kamfani mallakin abokinsa.

An ji muryar na cewa: “Ku yi abin da ya dace. Ku samar da kwangilar da ake buƙata, sannan ku ba wa kamfaninsa, domin mu rika biyan sa saboda ayyukan da yake yi.”

Da yake ƙarin bayani kan saƙon muryar, jami’in binciken EFCC, Christopher Odofin, ya shaida wa kotu cewa, kamfanin da ake magana a kai shine Tanaero Nigeria Limited (TNL), wanda ya ce mallakin Gabriel Tilmann ne, wanda ya bayyana a matsayin abokin tsohon ministan. Shaidar ta kuma ce, Sirika ya bayyana Tilmann a cikin saƙon a matsayin gogaggen matuƙin jirgi da kuma ƙwararren mai gudanarwa wanda ya taimaka wajen kafa kamfanonin jiragen sama da dama a sassan duniya, ciki har da ƙatar Airways.

An kuma ji Sirika yana cewa: “Duk abin da za mu iya samu daga gare shi, mutum ne mai ƙwazo da kuzari sosai… yana da duk abin da ake buƙata.”

Saƙon muryar ya kuma nuna cewa, Tilmann yana da kusanci da Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama saboda dangantakarsa da Sirika. An ji muryar tana cewa: “Saboda ni ne, yana jin daɗin mu’amala da ma’aikatar sosai.”

A yayin zaman kotun, Mista Michael Numa, lauyan kamfanin Al Buraƙ Investment, ya nuna rashin amincewa da wasu tambayoyin da masu gabatar da ƙara suka yi, yana mai cewa suna neman hasashe ne maimakon hujjoji. Sai dai Mai Shari’a Oriji ya shawarci ɓangaren masu kare wanda ake tuhuma da su adana ƙorafinsu har zuwa lokacin yi wa shaidar tambayoyi na ƙetare.

Lauyan ya kuma yi zargin cewa tambayoyin masu gabatar da ƙarar na da nufin jan hankalin kafafen yaɗa labarai maimakon tabbatar da gaskiya a gaban kotu.

Da yake mayar da martani, Mai Shari’a Oriji ya buƙaci lauyoyin kariya da kada su damu da rahotannin kafafen yaɗa labarai, sai dai su mayar da hankali kan gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Daga bisani, kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar Alhamis domin ci gaba da sauraron shaidu da gabatar da hujjoji.

By ukarofi