Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Wasu al’ummar ƙaramar Hukumar Mulki ta Dandi da ke Jihar Kebbi sun bayyana damuwarsu kan abin da suka bayyana a matsayin rashin ingantaccen wakilci daga ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Arewa/Dandi a Majalisar Wakilai ta Tarayya.
Daya daga cikin shugabannin matasa a yankin, Malam Hashimu Musa Buma, ya bayyana cewa akwai buƙatar sake nazari kan wakilcin Hon. Garba Rabi’u Kamba, wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Arewa da Dandi, yana mai zargin cewa wakilcin bai kai yadda al’umma ke tsammani ba.
Ya ce ya kamata a yi la’akari da ra’ayin jama’a da kuma ƙarfafa shugabanci mai kusanci da al’umma domin tabbatar da ci gaba da nasarar jam’iyya a yankin.
Hashimu Musa Buma ya kuma jaddada cewa yankin Kamba da kewaye na daga cikin wuraren da ake buƙatar tsayar da ’yan takara masu karɓuwa da nagarta domin samun nasara a zaɓe.
Ya ƙara da cewa akwai alamun damuwa a tsakanin wasu magoya bayan jam’iyyar APC a yankin Arewa/Dandi, musamman dangane da yadda suke kallon wakilcin da suke samu a halin yanzu.
A cewarsa, har yanzu akwai damar gyara da kuma ɗaukar matakan da suka dace domin ƙarfafa haɗin kai da tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓukan da ke tafe.
Ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su yi amfani da lokaci wajen nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa an tsayar da ’yan takara da za su samu cikakken goyon bayan al’umma.
Hashimu ya bayyana cewa siyasa na buƙatar haɗin kai, adalci da kuma aiki tukuru, yana mai cewa jama’a su ne mafi kyawun alkalai wajen tantance nagarta da ingancin shugabanci.
