
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗa wasu mutane 26 acikin hukumomin gwamnati da jagoranci 10 a hukumomin Gwamnatin Tarayya, inda tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose ya zama Shugaban Hukumar Samar da Lantarki a Yankunan Karkara (REA).
Haka kuma, ya naɗa Manjo-Janar Junaid Bindawa a matsayin shugaban Hukumar Kula da Harkokin Albashi, Kuɗaɗen Shiga da na Ƙwadago.
Rahotanni sun bayyana cewa, waɗannan naɗe-naɗe za su fara aiki ne a nan take, matakin da gwamnatin Shugaba Tinubu ta ɗauka don ganin ta inganta lamuran gudanar da harkokin gwamnati.
Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a wata takarda a ranar Litinin.
Ya ce, shugaban ƙasar ya kuma amince da naɗin Dakta Abuh Mohammed a matsayin Darakta Janar na Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Dakta Akinola Odeyemi a matsayin Manajan Darakta na Kamfanin Nigerian Bulk Electricity Trading (NBET), da Dr. Anthony Inalegwu Godwin a matsayin Shugaba kuma Babban Darakta na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Nijeriya.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya kafa sabon kwamitin Hukumar Kula da Da’a a Harkokin Kuɗaɗen Gwamnati (Fiscal Responsibility Commission), inda ya naɗa Dr. Abdullahi Maikano Saidu a matsayin shugaba tare da wasu mambobi shida.
Sannan ya naɗa Shuni Muhammad Dahiru a matsayin Babban Sakataren Hukumar Yaƙi da Jahilci da Ilimin Manya ta Ƙasa, yayin da Tosin Johnson Adeyanju ya koma mukamin Sakataren Hukumar Rabon Kuɗaɗen Shiga da Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi ta Ƙasa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Injiniya Julius Oloro ya zama Babban Daraktan Cibiyar Kera Kayan Aikin Noma ta Ƙasa (NCAM), yayin da Gisaor Vincent Iorja ya maye gurbin Mathias Byuan a matsayin Babban Daraktan Kuɗi na Hukumar Gidaje ta Tarayya (FHA), bayan murabus ɗin da magabacinsa ya yi domin neman takarar gwamna a Jihar Benuwai.
