
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar Sojin Nijeriya ta yi gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da ayyukan tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabas, bayan da wani babban jami’in kula da harkokin kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP tare da wasu yara maza guda biyu suka miƙa wuya ga dakarun Atisayen Haɗin Kai a Jihar Borno.
Rundunar sojin ta sanar da haka ne a wata takarda a ranar Asabar, inda ta bayyana cewa an samun babbar nasara a yaƙin da take yi da ta’addanci da kuma amfani da bayanan sirri wajen daƙile harkokin ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas.
Jami’in yaɗa labarai na Atisayen Haɗin Kai (OPHK), Kyaftin Mohammed Goni a sanarwar, ya bayyana cewa ɗan ta’addar ya miƙa wuya ne da misalin ƙarfe 6:45 na safiyar ranar Asabar ga jami’an Bataliya ta 3 ƙarƙashin 24 Task Force Brigade akan hanyar Ladari zuwa Jegarawa zuwa Tunokalia da ke yankin Gamboru zuwa Wulgo, inda nan ne mafi girman wajen da suke amfani da shi yayin raba kayayyakinsu.
A cewarsa, wannan ɗaya ce daga cikin muhimman nasarori da ‘yan OPHK suka samu da kuma ƙara matsin lamba ga ayyukan ƙungiyoyin ta’addanci a shiyyar.
Ya bayyana cewa, miƙa wuyan ya samu ne yayin da ‘yan ta’adda suke ƙoƙarin sauya sheƙa daga sansanoninsu, yana mai cewa kimanin ‘yan ta’adda 46 ne suka miƙa wuya tare da iyalansu a ‘yan kwanakin nan.
Ya ƙara da cewa, ana samun ire-iren nasarorin ne sakamakon atisayen dakarun tsaro ta sama da ƙasa a maɓoyar ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabashin Nijeriya.
