Matawalle ya umarci sojoji su ƙara ƙaimi bayan munanan hare-haren ‘yan ta’adda a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya bayyana ta’aziyya ga wadanda hare-haren ta’addanci ya shafa a Karamar Hukumar Bungudu da sauran al’ummomi a Jihar Zamfara. Haka kuma ya ba da umarnin a kara zafafa ayyukan soja a fadin yankin Arewa maso Yamma.

A cikin wata sanarwa da mataimakin sa na musamman kan harkokin yada labarai, Ahmed Dan Wudil, ya fitar ranar Lahadi, Dr. Matawalle ya ce Gwamnatin Tarayya na ci gaba da jajircewa wajen mayar da zaman lafiya da tsaro duk da karuwar hare-hare da aka samu a wasu sassan Arewa maso Yamma.

Ministan ya ba da umarni na musamman ga Rundunar Sojin Operation Fansan Yamma da su kasance masu kwazo da dagewa wajen yaki da ta’addanci, tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da aka tura yankunan da abin ya shafa.

Bugu da kari, ya umarci dakarun Soji na Operation Fansan Yamma da dukkan rundunonin soja da ke gudanar da ayyukan yakar ta’addanci da su kara kokari a jihohin Zamfara, Kebbi, Katsina, Sokoto da Kaduna.

A cewar sanarwar, an ba sojoji umarnin su dauki dukkan matakan da doka ta ba da dama domin kawar da ayyukan ta’addanci ta hanyar ayyukan yaki ba tare da tausayi ba.

Haka kuma ya umurci manyan kwamandojin soji da ke kula da yankunan da ke da matsaloli da su kara karfafa sa ido da yawaita sintiri da nufin gano da rusa maboyar ‘yan ta’adda, da mafaka su kafin su kai wasu hare-hare.

Matawalle ya yi kira ga jama’a, musamman sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, da su ba da hadin kai ga hukumomin tsaro ta hanyar ba da bayanan sirri cikin gaggawa.

Ya jaddada bukatar samun bayanai kan mutanen da ke taimaka wa ‘yan ta’adda ko hada baki da su, ciki har da wadanda ke ba da bayanai da ake amfani da su wajen kai hare-hare kan al’ummomin karkara.

Ministan ya yaba wa Sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro kan jarumtarsu, sana’a da sadaukarwarsu.

Ya kuma lissafa wasu nasarorin da aka samu kwanan nan na kawar da ‘yan ta’adda da dama manya da kanana a Gummi, Bukkuyum, Anka, Tsafe, Faskari da sauran wurare a fadin yankin.

A karshe ya bukaci sojoji da su ci gaba da wannan kwazo da matsa kaimi har sai an fatattaki ta’addanci gaba daya a duk sassan kasar.

By Babaji

Leave a Reply