Sojoji sun ceto mutum 14 da aka sace a babban titin Legas zuwa Benin

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro na Birget ta 4 na Rundunar Sojin Nijeriya da ke Sashe na 2, sun yi nasarar ceto wasu mutane su 14 da aka yi garkuwa da su a yankin babban titin Legas zuwa Benin a Ƙaramar Hukumar Ovia ta Gabas da ke Jihar Edo, a wani ɓangare na Atisayen Wabaizigan.

A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Kennedy Anyanwu ya aike wa manema labarai, ya ce an gudanar da atisayen ne bayan al’amarin garkuwar ya faru da misalin ƙarfe 9:30 na daren Alhamis, 30 ga Yuli, 2026.

Ya ce, dakarun da ke sintiri sun samu wani bayani na sirri kan al’amarin, lamarin da ya sa cikin hanzari suka bi sawun ‘yan bindigar da suka sace mutanen. A yayin haka ne suka sako 11 daga cikinsu tare da tserewa zuwa bayan gari.

A washe gari ne kuma dakarun suka sake komawa farauto ‘yan bindigar da ƙoƙarin ceto sauran mutanen, lamarin da ya sa suka yi nasarar ceto mutum uku kuma jimillar waɗanda aka ceton ta kai 14.

A cewar hukumomin soji, baki ɗaya mutanen sun samu kulawar da ta dace kuma an tabbatar da kasancewarsu cikin ƙoshin lafiya kana daga bisani aka haɗa su da iyalansu ko suka cigaba da tafiyarsu.

Rundunar ta ƙara da cewa, an baza komar neman ‘yan bindigar da suka tseren da kuma ƙoƙarin kamo dukkan masu hannu acikin aikata laifin, tana mai bayyana matakin a matsayin ƙoƙarin dakarun tsaron na daƙile ayyukan garkuwa da ta’addanci a Nijeriya da haɗin-gwiwar sauran hukumomin tsaro.

Kazalika, ta yi kira ga jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaron bayanan da za su taimaka musu akan lokaci a ƙoƙarinsu na inganta tsaro a sassan Jihar Edo da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji