Daga GAMBO ISA a Abuja
Mai Martaba Sarkin Machina, Alhaji (Dr.) Bashir Albishir Bukar Machinama (OON, L’ONN), ya kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Agadez (Sultan d’Aïr) da kuma Shugaban Hukumar Gudanarwar Birnin Agadez, Chef de Bataillon Assarid Almoustapa, Administrateur Délégué (AD), a Jamhuriyar Nijar.
Ziyarar, wadda aka gudanar a ranar Laraba, 5 ga Agustan 2026, na da nufin ƙara ƙarfafa zumunci, haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin masarautun gargajiya, tare da bunƙasa dangantakar tarihi da ta daɗe tsakanin al’ummar Tarayyar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar tun daga zamanin Daular Kanem-Borno.
A yayin ziyarar, Mai Martaba Sarkin Machina ya jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin kai, zaman lafiya da haɗin gwiwa tsakanin sarakunan gargajiya na ƙasashen biyu domin ƙarfafa zaman tare cikin lumana, kare al’adun gargajiya da kuma bunƙasa ci gaban al’umma.
Ya ce dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da Nijar ta samo asali ne tun shekaru masu yawa da suka gabata, don haka akwai buƙatar ci gaba da kare wannan kyakkyawar alaƙa domin amfanin al’ummomin ƙasashen biyu.
Sarkin ya kuma gode wa Sarkin Agadez da Shugaban Hukumar Birnin Agadez bisa kyakkyawar tarbar da suka yi masa da tawagarsa, yana mai tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da ƙarfafa dangantakar tarihi da ke tsakanin al’ummar Nijeriya da Nijar.
Sanarwar ta fito ne daga Sakataren Yaɗa Labarai na Masarautar Machina, Ibraheem Kachallah Macheena.
