Kwamishinan Gombe ya ƙaddamar da sabon tsarin sa ido kan ƙananan hukumomi

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Kwamishinan ma’aikatar ƙananan hukumomi da raya al’umma ta Jihar Gombe, Barrista Sani Ahmed Haruna, ya ƙaddamar da wani sabon tsari na sa ido kan ayyukan ƙananan hukumomi, inda ya umarci sashen bincike, saka Ido da tantance ayyuka na ma’aikatar da ya riƙa gabatar da rahotannin bincike a duk wata.

Ya bayyana cewa matakin na da nufin ƙarfafa sa ido kan yadda ƙananan hukumomi ke gudanar da ayyukansu, bunƙasa gaskiya da riƙon amana, tare da inganta isar da ayyukan gwamnati ga al’umma.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin taronsa na farko da ma’aikatan sashen, inda ya kuma umarce su da su inganta tsarin adana bayanai domin tabbatar da cewa ana tattarawa da adana dukkan rahotannin bincike cikin tsari.

A cewarsa, an maye gurbin tsarin gabatar da rahoto duk bayan watanni uku da na kowane wata ne domin bai wa ma’aikatar damar bibiyar ayyukan ƙananan hukumomi a kai a kai, gano matsalolin da ke tasowa cikin lokaci da kuma ɗaukar matakan gyara cikin gaggawa.

“Rahoton kowane wata zai ba mu cikakken bayani kan halin da ƙananan hukumomi ke ciki, tare da taimaka wa ma’aikatar ɗaukar matakan da suka dace domin inganta ayyukan gwamnati,” in ji shi.

Barrista Haruna ya bayyana sashen bincike, saka ido da tantance ayyuka a matsayin ginshiƙin ma’aikatar, yana mai cewa kusan kashi 70 cikin 100 na manyan ayyukan ma’aikatar na ƙarƙashin wannan sashe ne.

Ya buƙaci jami’an sashen su gudanar da aikinsu cikin ƙwazo, ƙwarewa da riƙon amana, yana mai jaddada cewa sa ido mai inganci da kuma gabatar da rahotanni cikin lokaci na da muhimmiyar rawa wajen inganta shugabanci a matakin ƙananan hukumomi.

Har ila yau, ya sake jaddada aniyarsa ta gina ma’aikata mai mayar da hankali kan sakamako, gaskiya, riƙon amana da kuma ingantacciyar hidima ga al’umma.

Da yake nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Shuaibu Ibrahim, ya yaba wa kwamishinan bisa salon jagorancinsa na buɗaɗɗiyar ƙofa, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa haɗin kai tsakanin ma’aikata, inganta sadarwa da kuma bunƙasa gaskiya a harkokin ma’aikatar.

Shi ma daraktan ƙananan hukumomi, Alhaji Musa Idi Batari, ya bayyana cewa sashen bincike, saka ido da tantance Ayyuka ne ke kula da binciken ayyukan ƙananan hukumomi, sanya ido kan aiwatar da shirye-shiryen gwamnati, tantance yadda ake gudanar da su da kuma tabbatar da bin manufofi da ƙa’idojin gwamnati.

A ƙarshe ma’aikatan sashen sun tabbatar wa kwamishinan da cikakken haɗin kai wajen aiwatar da sabon tsarin sa ido da gabatar da rahotanni, domin ƙarfafa gudanar da ƙananan hukumomi da inganta ayyukan gwamnati a faɗin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply