Ku bar ’yan Nijeriya su ji ta bakina – Shugaban hukumar bogi ya nemi majalisa ta zauna da shi a bainar jama’a

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mutumin da ake zargi da ƙirƙira tare da jagorantar Hukumar Majalisar Shugaban ƙasa kan Bunƙasa Zuba Jarin ƙasashen Waje (PFIPC) ba ta halastacciyar hanya ba, Mista Adeniyi Adeyemi, ya yi fatali da shirin Kwamitin Wucin Gadi na Majalisar Wakilai na yi masa tambayoyi a wani wuri da ba a bayyana ba, yana mai cewa, ya kamata a saurare shi a bainar jama’a, domin ‘yan Nijeriya su ji abin da zai faɗa.

Adeyemi, wanda ke tsare a hannun Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, ya bayyana matsayarsa ne ta bakin lauyansa, Ademola Oyedokun, a ranar Laraba.

Lauyan ya ce, duk da cewa wanda yake karewa yana maraba da binciken da majalisar ke yi kan yadda aka kafa da kuma ayyukan hukumar ta PFIPC, bai amince da a yi masa tambayoyi a ɓoye ba.

A cewarsa, tunda duk waɗanda suka yi zarge-zarge a kansa sun yi hakan ne a zaman sauraron jama’a da kwamitin ya gudanar, adalci ya tanadi a ba shi damar kare kansa a irin wannan zama.

“Mun samu labarin cewa kwamitin na shirin yi wa wanda muke karewa tambayoyi a wani lokaci da kuma wurin da ba a bayyana ba. Muna roƙon kwamitin da ya sake nazarin wannan matsaya.

“Duk waɗanda suka bayyana a wannan batu sun yi magana ne a bainar jama’a, kuma duk abin da aka faɗa a kansa a fili aka faɗa. Don haka ya kamata shi ma a ba shi damar mayar da martani a fili.”

Oyedokun ya buƙaci kwamitin ya yi amfani da ikon da Sashe na 89 na Kundin Tsarin Mulkin Nujeriya ya ba shi wajen umartar ‘yan sanda su gabatar da Adeyemi a gaban zaman sauraron jama’a.

Ya ce wanda yake karewa zai halarci zaman tare da lauyansa kuma zai amsa duk tambayoyin da kwamitin zai yi masa.

Sai dai ya bayyana cewa duk wasu tambayoyin da suka shafi shari’ar da ke gaban kotu ko hukumomin bincike za a bari a amsa su a wuraren da suka dace.

Oyedokun ya ce, ba sa neman kwamitin ya dakatar da binciken da ake yi, amma suna son a ba Adeyemi damar yin bayani kan yadda PFIPC ta samu wanzuwa da kuma waɗanda ke cikin gwamnati suka yi hulɗa da ita. Ya ce wannan batu ne da ya dace ‘yan Nijeriya su ji amsarsa kai tsaye.

“Babu wata kotu da ta saurari bayanin wanda muke karewa har yanzu. Saboda haka ya kamata jama’a su ji abin da zai faɗa da kunnuwansu,” inji shi.

Lauyan ya kuma yi zargin cewa ci gaba da tsare Adeyemi ba ya da tushe a doka. A cewarsa, sammacin da kotu ta bayar ya ba da izinin kama shi da gabatar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya ne kawai, ba tare da ba da umarnin ci gaba da tsare shi ba.

A ranar Talata ne Kwamitin Wucin Gadi na Majalisar Wakilai mai bincike kan zargin kafa da gudanar da PFIPC ya sanar da cewa zai yi wa Adeyemi tambayoyi a wani wuri da ba a bayyana ba yayin da yake tsare.

Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin kada a kawo cikas ga binciken da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) da kuma Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC) ke gudanarwa.

Ya ƙara da cewa, majalisar ba za ta ɗauki wani mataki da zai saɓa wa umarnin kotu ko ya karya ƙa’idar rabon iko tsakanin sassan gwamnati ba.

Kwamitin na bincike ne kan zarge-zargen da suka haɗa da kafa PFIPC ba bisa ƙa’ida ba, yin sojan gona, ƙirƙirar takardun bogi, taɓargazar kuɗi, da kuma amfani da tambura da kadarorin gwamnati ba tare da izini ba.

By ukarofi