(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
Duk lokacin da wani fitaccen mutum daga masana’antar nishaɗi ya shiga siyasa, tambayar da jama’a ke yi ba ta tsaya kan ko zai iya lashe zaɓe ba. Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne: me ye nufinsa na shi siyasa?
Shin ya je ne domin ya wakilci muradun mutanen da suka ba shi suna, ko kuwa ya yi amfani da shahararsa ne domin ya buɗe wa kansa wata sabuwar ƙofa?
Wannan tambaya ba ta Kannywood kaɗai ba ce.
Nollywood ma ta sha ganin fitattun jarumanta suna shiga harkokin siyasa, wasu kai tsaye ta hanyar neman kujeru, wasu kuma ta hanyar tallafa wa ‘yan takara ko karɓar muƙaman gwamnati.
Abin da tarihin wasu daga cikinsu ya nuna shi ne cewa shahara na iya buɗe ƙofar siyasa, amma ba ita ce ke tabbatar da mutum a cikinta ba.
A shekarar 2014, jarumar Nollywood Kate Henshaw ta shiga takarar kujerar Majalisar Wakilai a ƙarƙashin PDP, amma ta rasa tikitin jam’iyyar a zaɓen fidda gwani. Duk da rashin nasarar, hakan bai sa ta rufe ƙofar da ta fito daga cikinta ba.
Ta ci gaba da aikin fim, ciki har da fitowarta a fim ɗin nan mai suna ‘Roti’, wanda aka fitar a 2017. Wannan misali ya nuna cewa shiga siyasa da rashin nasara ba lallai ne ya zama ƙarshen aikin fasaha ba.
Haka kuma, Dayo Adeneye ya taɓa neman tikitin APC na kujerar Majalisar Dokokin Ogun, kafin daga bisani ya koma wani matsayi a gwamnati. Wannan ya sake nuna yadda rayuwar mai fasaha da siyasa za su iya haɗuwa ba tare da ɗaya ya zama ƙarshen ɗayan ba.
Darasin da ke fitowa daga irin waɗannan misalai shi ne, cewa siyasa na iya zama wani sashe na rayuwar mai fasaha, ba dole ta zama abin da zai goge asalinsa na sana’a gaba ɗaya ba.
Amma a Kannywood, batun ya fi haka zurfi. Domin Kannywood ba ta fara siyasa jiya ba, kuma shigar ‘yan Kannywood cikin siyasa ba sabon abu ba ne.
Tun shekaru da suka gabata, wasu daga cikin fitattun jarumai sun nemi muƙamai daban-daban na siyasa. Hamisu Lamido Iyantama ya tsaya takarar gwamnan Kano a 2007, yayin da wasu daga cikin fitattun masu ruwa da tsaki a masana’antar suka nemi muƙamai a matakan tarayya da jihohi. Wasu sun ci gaba da neman mukami, wasu kuma suka koma harkar fim bayan rashin nasara.
Sai dai a ‘yan shekarun nan, dangantakar Kannywood da siyasa ta wuce batun mutum ɗaya da ya tsaya takara.
Masana’antar ta zama ɗaya daga cikin hanyoyin da ‘yan siyasa ke amfani da su wajen isar da saƙonnin yaƙin neman zaɓe.
Jarumai da mawaƙa da dama sun shiga gangamin ‘yan siyasa, sun yi waƙoƙi, gajerun fina-finai da sauran saƙonnin yaƙin neman zaɓe.
Binciken da jaridar Daily Trust ta taɓa fitarwa ya bayyana cewa, Kannywood ta taka rawa wajen tallafa wa yaƙin neman zaɓen Muhammadu Buhari a zaɓukan 2015 da 2019, yayin da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a masana’antar suka shiga cikin yaƙin neman zaɓen kai tsaye.
A zaɓen 2023 ma, binciken ya nuna cewa ‘yan Nollywood sun fi takwarorinsu na Kannywood yawa wajen neman kujerun zaɓe, duk da cewa duka masana’antun biyu sun ci gaba da taka rawa wajen tallafa wa ‘yan takara.
Wannan ya ba masana’antar wani irin ƙarfi a siyasa da ba za a iya watsi da shi ba. Amma duk inda tasiri irin na siyasa yake, akwai tambayar ko akwai hamayya.
Lokacin da siyasa ta shiga cikin masana’antar fim a nan ne labarin Kannywood ya fi rikitarwa. Domin siyasar ba ta shafi jarumin da ya shiga takara kaɗai ba. Tana iya shafar masana’antar gaba ɗaya.
Lokacin da masu fasaha suka rarrabu tsakanin jam’iyyu da ‘yan takara, bambancin ra’ayin siyasa na iya shiga cikin dangantakar da ke tsakanin masu ruwa da tsaki a masana’antar.
Binciken Daily Trust kan dangantakar Kannywood da siyasa ya nuna cewa masana’antar ta taɓa fuskantar irin wannan rarrabuwar kai musamman a lokutan zaɓe, yayin da wasu ke kallon siyasa a matsayin hanyar kai buƙatun masana’antar ga gwamnati, wasu kuma ke ganin kusancin da ‘yan siyasa zai iya raba masana’antar zuwa ɓangarori.
Wannan ba ƙaramin abu ba ne. Domin idan jarumi ya goyi bayan ɗan takara, shahararsa na iya ba wa ɗan siyasar damar isa ga wani ɓangare na jama’a da ba lallai ne ya samu sauƙin isa gare su ba. Amma idan wannan kusanci ya koma neman alfarma ko fifita wani ɓangare, sai wata tambaya ta taso: Ina amfanin masana’antar yake ƙarewa, ina kuma amfanin mutum yake farawa?
A gefe guda kuma, gwamnati na iya amfani da ƙwarewar masu fasaha wajen tsara manufofin da suka shafi masana’antar nishaɗi.
A shekarar 2024, an naɗa Ali Nuhu a matsayin Manajan Darakta na Nigerian Film Corporation. Daga baya kuma, aka naɗa Rahama Sadau cikin kwamitin fasaha na shirin Investment in Digital and Creative Enterprise, wato iDICE.
A watan Disambar 2024 kuma, Gwamnan Kano Abba Yusuf ya naɗa Sani Danja a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan matasa da wasanni.
Waɗannan misalai suna nuna wani muhimmin ɓangare na alaƙar masana’antar nishaɗi da gwamnati: wani lokaci shiga tsarin gwamnati ba sai mutum ya tsaya takarar zaɓe ba.
