Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yan takarar shugaban ƙasa da shugabannin wasu jam’iyyun siyasa sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta ƙasa domin gudanar da kamfen na zaɓen 2027 cikin lumana, tare da yin watsi da tashin hankali, kalaman ƙiyayya, yaɗa labaran ƙarya da tayar da zaune tsaye kan kabilanci ko addini.
An rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata a Abuja, ƙarƙashin jagorancin kwamitin zaman lafiya na ƙasa wato National Peace Committee (NPC) tare da haɗin gwiwar The Kukah Centre, gabanin fara kamfen ɗin zaɓen 2027 a ranar Laraba, 19 ga Agusta.
Sai dai wasu manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa, ciki har da ɗan takarar APC, Shugaba Bola Tinubu, da ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, ba su halarci taron ba. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ne ya wakilci Tinubu.
Daga cikin ‘yan takarar da suka halarta akwai Peter Obi na NDC, Adewole Adebayo na SDP da Omoyele Sowore na AAC.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce yarjejeniyar ta zo a daidai lokacin da ya dace, inda ya tunatar da cewa zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya zai gudana a 16 ga Janairu 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da majalisun jihohi zai gudana a 6 ga Fabrairu 2027.
Amupitan ya bukaci ‘yan siyasa su mayar da kamfen kan manufofi da hanyoyin magance matsalolin Nijeriya, maimakon kai hare-haren kashin kai, kalaman ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.
Ya ce zaɓe ba yaƙi ba ne, yana mai bayyana shi a matsayin gasa tsakanin ‘yan takara domin samun amanar masu zaɓe.
Shi kuwa Peter Obi ya ce ya kamata ‘yan Nijeriya su hukunta duk ɗan takara ko jam’iyyar da ta karya yarjejeniyar ta hanyar ƙin zaɓensu.
Kwamitin Zaman Lafiya ya bayyana cewa yarjejeniyar ba wata takarda ce ta biki kawai ba, domin tana da tushe a Kundin Tsarin Mulki, Dokar Zaɓe da ƙa’idojin INEC.
Kwamitin ya kuma bayyana cewa ya samu rahoto 2,510 na matsalolin tsaro tsakanin Yuni 2025 zuwa Agusta 2026, tare da wasu ɗaruruwan laifukan zaɓe.
An buƙaci jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, kafafen yaɗa labarai, hukumomin tsaro, shugabannin addinai da na gargajiya su taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da gudanar da kamfen cikin mutunci.
Hukumar ‘yan sanda ta kuma yi gargaɗi ga jam’iyyu da magoya bayansu kan amfani da ‘yan daba, makamai, barazana ko kalaman tunzura jama’a yayin kamfen.
