Shekaru 131 kenan tun bayan da al’ummar Kano suka tsinci kansu cikin mummunan yaƙin basasa sakamakon rikicin sarauta tsakanin gidan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi da gidan Sarkin Kano Muhammadu Bello, waɗanda dukkansu ‘ya’yan Sarkin Kano Ibrahim Dabo ne.
Masana tarihi sun bayyana wannan yaƙi a matsayin mafi muni da birnin Kano ya taɓa fuskanta. An rawaito cewa wani Bature da ya ziyarci Kano a lokacin ya ce, “Kano ta zama ƙasar jini saboda irin yawan jinin da aka zubar.” Wannan yaƙi ya haifar da babbar asara ga rayuka, dukiyoyi da kuma tattalin arzikin birnin.
Asalin rikicin:
Bayan rasuwar Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ɗansa Usman ya gaje shi. Bayan rasuwar Usman kuma, ƙanensa Abdullahi Maje Karofi ya zama Sarki. Da shi ma ya rasu, sai wani ƙanensu Muhammadu Bello ya hau karagar mulki.
Lokacin da Sarkin Kano Bello ya rasu a watan Disambar 1893, Wazirin Sakkwato Buhari yana Kano. Ya sanar da Sultan Abdurrahman rasuwar Bello, kuma Sultan ya naɗa Tukur, ɗan Bello, a matsayin sabon Sarkin Kano ba tare da bin cikakkiyar hanyar zaɓen da aka saba ba.
Wannan mataki ya jawo rashin amincewar yawancin manyan Kano, waɗanda suke goyon bayan Yusuf, ɗan Abdullahi Maje Karofi. Daga nan ne aka samu rabuwar kai tsakanin Tukurawa da Yusufawa.
Hijirar Yusufawa:
Magoya bayan Yusuf sun bar Kano tare da iyalansu, bayinsu da makamansu, suka kafa sansani a Takai, inda suka naɗa Yusuf a matsayin Sarkinsu. Daga nan suka fara neman mubaya’a daga garuruwa domin su dawo su ƙwace mulkin Kano.
A watan Agustan 1894 suka nufi Kano, amma Yusuf ya rasu a garin Garko kafin su isa. Kafin rasuwarsa, an ce ya bayyana cewa a naɗa ɗan uwansa Alu (Aliyu Babba) a matsayin magajinsa.
Naɗin Sarki Alu:
Bayan rasuwar Yusuf, aka naɗa Sarki Alu (Alu Babba ko Alu Maisango). A ranar 18 ga Satumba, 1894, Alu ya jagoranci rundunar Yusufawa zuwa Kano domin ƙwace mulki daga hannun Sarki Tukur.
Sarki Tukur da magoya bayansa suka fice daga Kano zuwa yankin Katsina domin neman mafaka da taimako. Sultan Abdurrahman ya nemi sarakunan Zazzau, Katsina da Kazaure su taimaka wa Tukur, amma ba su amince ba.
A watan Maris 1895, rundunonin Alu da Tukur suka gwabza a Tafashiya. Alu ya yi nasara, yayin da Tukur ya ji munanan raunuka bayan faɗuwar dokinsa. Bayan wasu kwanaki yana jinya, Tukur ya rasu a ranar 16 ga Maris, 1895, lamarin da ya kawo ƙarshen yaƙin basasar Kano.
Illolin Yaƙin Basasar Kano:
Yaƙin ya haifar da manyan illoli, ciki har da mutuwar dubban mutane da zubar da jini mai yawa.
Hijirar iyalai da dama daga Kano zuwa ƙauyuka da sauran yankuna.
Lalacewar tattalin arzikin Kano da durƙushewar kasuwanci.
Bacewar mutane da dama ba tare da an san inda suka shiga ba.
Samuwar rabuwar kai tsakanin gidajen sarauta.
Wasu magada sun ƙi karɓar sarauta saboda abin da kakanninsu suka sha a lokacin yaƙin.
Masarautar Sakkwato ta ware Sarki Alu duk da dangantakar jini da ke tsakaninsu.
Turawan mulkin mallaka sun fahimci raunin Daular Usmaniyya da rarrabuwar kanta, abin da ya taimaka musu wajen mamaye Kano da sauran yankuna.
Wane ne Sarki Alu?
Sarki Alu, wanda ake kira Alu Maisango, ya mulki Kano daga 1895 zuwa 1903.
Ta wajen uba, Alu ɗan Abdullahi Maje Karofi, jikan Sarkin Kano Ibrahim Dabo ne. Ta wajen uwa kuma, jika ne ga Sultan Sarkin Musulmi Alu Babba ne, shi Alu Maisango ɗan Saudatu ne ‘yar Alu Babba. wanda ya fito daga zuriyar Shehu Usmanu ɗanfodiyo.
An san Alu a matsayin malami kuma jarumi. Yana amfani da wani makami da ake kira Sango, wanda ya sa aka yi masa laƙabin Maisango.
Zuwan Turawa da ƙarshen mulkinsa:
Bayan an naɗa Sultan Attahiru, Sarki Alu ya je Sakkwato domin yi masa mubaya’a. A hanyarsa ta dawowa Kano ne ya samu labarin cewa Turawan mulkin mallaka sun shiga Kano.
Sarki Alu ya yi yunƙurin tafiya gabas domin kauce wa Turawa, amma aka kama shi, aka kai shi Adamawa, daga bisani kuma aka mayar da shi Lokoja, inda ya rayu har zuwa rasuwarsa a shekarar 1926.
Naɗin Sarki Abbas:
Bayan kama Sarki Alu, Wamban Kano Abbas ya koma Kano tare da magoya bayansa. Turawan mulkin mallaka suka naɗa shi a matsayin Sarkin Kano a watan Fabrairun 1903, wanda hakan ya fara sabon babi na mulkin mallaka a Kano.
Kammalawa
Yaƙin Basasar Kano na 1894–1895 ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka sauya alkiblar tarihin Kano. Ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi, ya raunana Masarautar Kano da Daular Usmaniyya, sannan ya share fagen mamayar Turawan mulkin mallaka a shekarar 1903.
Allah Ya ƙara ɗaukaka Jihar Kano, harshen Hausa, da ƙasar Nijeriya baki ɗaya. Amin
