Gwamnatin Trump ta dakatar da bada bizar Amurka ga kowacce ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amurka ta dakatar da bayar da baki ɗaya bizar shiga ƙasarta ga masu buƙata yayin da ofisoshin jakadancinta suka fara bada sabon horo ga jami’an harkar jakadanci.

Fadar shugaban ƙasar ne ta tabbatar da haka a ranar Talata, inda ta ce za a yi gyara kan waɗanda suke aiki akansu domin bai wa ofishin difulomasiyyarsu damar shiga horon.

Gwamnatin ta kuma ce, matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarinta akan ƙarfafa ayyukan tantancewa da inganta tsaron ƙasar. Wani kakakin fadar ya ce aikin horon zai taimaka wa jami’an ofisoshin jakadanci yin nazari mai zurfi kan masu buƙatar biza kuma cikin ingantaccen tsari.

Saidai, fadar ba ta bayyana adadin lokacin da horon zai ɗauka ba ko kuma lokacin da za koma aikin bayar da bizar. Financial Times ce ta fara ruwaito batun dakatarwar, inda ta ce wasu da suka miƙa buƙatarsu ta samun biza da aka shirya tantance su da ofishin jakadancin ƙasar, sun samu saƙonnin Imel da ke cewa an sauya tsarin haɗuwar tantancewarsu.

Fadar Shugaban ƙasar dai ta kare wannan mataki, inda ta ce an yi hakan ne don tabbatar da cewa waɗanda suke ƙoƙarin neman bizar ba suna yi ne don dogara da abin da aka tanada ba ne domin amfanin ainihin ‘yan ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply