INEC ta tabbatar da Bilyaminu Shinkafi a matsayin ɗan takarar gwamnan ADC a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta tabbatar da Hon. Bilyaminu Aliyu Shinkafi a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar Zamfara kafin babban zaɓen 2027.

Sunan Shinkafi ya bayyana a cikin jerin ‘yan takarar ƙarshe da aka liƙa a ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa da ke Gusau, babban birnin jihar, ranar Asabar.

Wannan ci gaban ya nuna ƙarshen rikicin cikin gida da ya mamaye ADC a jihar yayin da shugaban jam’iyyar na jiha, Surajo Garba Gusau, ya sanar da Hon. Ibrahim Salisu Mafara a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar kwanaki biyu da suka gabata.

Sakamakon amincewar hukumar zaben INEC, Shinkafi yanzu zai ɗaga tutar ADC kuma zai fafata da Gwamna Dauda Lawal na APC, tare da sauran ‘yan takara daga Jam’iyyun NDC, AA, PRP da sauran jam’iyyun siyasa.

Da yake magana da wakilinmu a wata hira ta wayar tarho, Hon. Bilyaminu Shinkafi ya yaba wa INEC saboda bin ƙa’ida da bin doka.

Ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da mambobin ADC a Zamfara da su ajiye bambance-bambancenu su yi aiki tare don samun nasarar jam’iyyar a 2027.

“Ina yaba wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC saboda yin abin da ya dace. Wannan nasara ce ga dimokuradiyya da kuma iyalan ADC a Zamfara”. Ya ce

“Ina kira ga dukkan membobinmu da su rungumi haɗin kai da ci gaba domin mu samu nasara ga jam’iyyar a 2027.”

Masu lura da harkokin siyasa a Jihar sun lura cewa warware rikicin shugabancin ADC ya share hanyar da jam’iyyar za ta fara gangamin yakin neman zaɓe kafin zaɓen gwamna a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply