Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi kira ga mahalarta taron shawarwari kan kasafin kuɗi da su bayar da shawarwari masu amfani wajen tantance ayyuka da shirye-shiryen da ya kamata a bai wa fifiko a kasafin kuɗin shekarar 2027.
Kwamishinan ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki a jihar Alhaji Ahmed Yakubu Mohammed ne yayi wannan kiran a yayin taron tattaunawa na musamman da al’umma kan kasafin kuɗin ‘yan ƙasa na 2026 wato Citizens Budget a turance wanda aka gudanar a ɗakin taro na hukumar bunƙasa zuba jari ta Jihar Nasarawa (NASIDA) da ke kan titin Shendam a Lafia babban birnin jihar.
Taron mai taken “Ƙarfafa shigar al’umma da bayyana gaskiya da riƙon amana a tsarin kasafin kuɗi,” ya samu halartar ƙungiyoyin farar hula da abokan cigaba da sarakunan gargajiya da shugabannin addini da ‘yan jarida da ‘yan kasuwa masu zaman kansu da ƙungiyoyin mata da matasa da wakilan al’ummomi da sauran masu ruwa da tsaki.
Mohammed yace “Halartarku na nuna ƙuduri na bai ɗaya don tabbatar da cewa kasafin kuɗin Jihar Nasarawa ya cigaba da dacewa da buƙatu da muradu da kuma fifikon al’ummarta.
“A matsayinku na masu cin gajiyar kashe kuɗaɗen gwamnati kai tsaye ‘yan ƙasa na da muhimmiyar rawa a tsarin kasafin kuɗi. Shigarku zai taimaka wa gwamnati ta fahimci buƙatun al’ummomi tare da tabbatar da cewa an tura haƙƙin jama’a zuwa ayyukan da za su kawo babban tasirin cigaba.
“Tun bayan fara taron shawarwari da al’umma kan kasafin kuɗi a jihar Nasarawa a shekarar 2025 mun samu gagarumin cigaba wajen tabbatar da cewa ba a kallon tsara kasafin kuɗi a matsayin al’amari na gwamnati kaɗai daga sama ba maimakon haka muna canza shi a hankali zuwa wani tsari na fili mai bayyana gaskiya da na shigar al’umma inda muryoyi da buƙatu da muradun al’umma ke bayar da gudummawa ga tsare-tsare kasafin kudi da aiwatarwa.”
Ya ƙara da cewa wannan tsarin ya haifar da sakamako mai kyau a shekarar 2025 inda aka amince da dama daga cikin ayyuka da shirye-shiryen da al’umma suka bayar da shawarar kuma an aiwatar da su ko kuma ana kan aiwatar da su tun daga gina da gyaran hanyoyi a karkara da samar da ruwan sha mai tsafta da kayayyakin aikin gona da ababen more rayuwa na ilimi dana kiwon lafiya.
Shima da yake jawabi a wajen taron daraktan kasafin kuɗi da tsare-tsare na ma’aikatar Mista Akolo Peters ya bayyana kasafin kuɗi a matsayin ɗaya daga cikin muhimman kayan aikin da gwamnati ke amfani da su wajen mayar da fifikon cigabanta da manufofi da shirye-shiryenta zuwa ayyuka na zahiri da za su amfanar da al’umma.
Peters ya jero manufofin taron da suka haɗa da wayar da kan al’umma game da tsarin kasafin kuɗi da zagayowar kasafin kuɗi na jihar da bayyana fifikon cigaban gwamnati da yadda ake rabon kasafin kudi da bai wa al’umma damar bayar da gudummawa wajen tsara fifiko da samun ra’ayoyin al’umma kan shirye-shiryen gwamnati da inganta bayyanan gaskiya da riƙon amana wajen sarrafa albarkatun jama’a da ƙara fahimtar al’umma kan kasafin kuɗin ‘yan ƙasa da gano manyan buƙatun cigaba a al’ummomi da sassa daban-daban da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma da ƙungiyoyin farar hula da abokan cigaba.
Wakilan mahalarta taron daga ƙungiyoyi daban-daban sun yaba wa ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare da gwamnatin jihar bisa samar musu da wannan damar bayyana ra’ayoyinsu kafin aiwatar da kasafin kudin tare da yin kira da a cigaba da irin wannan taron.
