
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dawo Nijeriya a ƙarshen makon nan bayan ƙarin wa’adin hutunsa da ‘yan kwanaki.
A ranar 30 ga watan Agusta ne Tinubu ya bar Nijeriya zuwa Landon domin fara hutunsa na shekara, inda daga bisani ya garzaya Paris a ƙasar Faransa ya cigaba da harkokinsa yayin da kuma yake shiga lamuran gida Nijeriya daga can. Kakakinsa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026.
Bayan shafe mako guda a Landon, Tinubu ya je Paris inda ya gana da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da Attajiri Mista Vincent Bollore, wanda kafafensa na labarai suka haɗa da Canal+, Multichoice da Universal Music Group.
Duk da cewa Shugaban yana hutu, amma ya cigaba da kula da wasu harkokin gida, ciki har da umartar kwamiti mai zaman kansa da ya yi bincike kan mutuwar masu haƙar ma’adinai ba bisa doka ba guda 37 a Minna, bayan jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun tsare su da kuma wasu harkoki daban-daban.
Haka kuma, Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da ya wakilce shi a wasu muhimman al’amura, ciki har da a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
