Gwamnatin Tarayya ta bada tallafi na kuɗi ga mutane 8,261 ƙarƙashin CCT a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An ƙaddamar da shirin bayar da tallafin kuɗi na gwamnatin tarayya na Conditional Cash Transfer (CCT), karo na tara ga mutane 8,261 a ƙananan hukumomin Mashi da Ingawa na jihar Katsina.

Da yake jawabi, shugaban shirin na ƙaramar hukumar Mashi, Alhaji Aminu Mashi ya bayyana cewa za a raba tallafin ga mazaɓu uku cikin kwanaki uku, wato Juma’a, Asabar da Lahadi.

Shi ma shugaban shirin na ƙaramar hukumar Ingawa, Ibrahim Mamman, a nasa jawabin, ya yi kira ga waɗanda za su amfana da shirin da su bi dokoki da ƙa’idojin da aka gindaya domin samun cikakkiyar fa’ida daga tallafin.

Ya kuma bayyana cewa duk wanda ya fuskanci wata matsala ko kuma akwai wani abu da bai fahimta ba a yayin rabon tallafin, ya tuntuɓi ma’aikatan shirin ko masu taimaka musu domin samun mafita.

A nasa jawabin, shugaban shirin na Jihar Katsina, Alhaji Aminu Alhassan, ya ce sun je ƙananan hukumomin Mashi da Ingawa ne domin ci gaba da aiwatar da shirin bayar da tallafin kuɗi na gwamnati kamar yadda aka saba.

Ya bayyana cewa mutane 2,150 ne za su amfana a ƙaramar hukumar Mashi, yayin da mutane 6,111 za su amfana a ƙaramar hukumar Ingawa, wanda jimillar su ta kai mutane 8,261.

Aminu Alhassan ya ce shirin an samar da shi ne domin tallafa wa al’umma da rage musu matsalolin rayuwa, inda ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina da kuma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon bayan da suke bai wa shirin.

Ya kuma bayyana yadda mata ke amfani da tallafin wajen taimaka wa mazajensu da iyalansu, yana mai cewa tallafin ba na ‘yan wata jam’iyya ba ne, illa tallafi ne da aka tanada domin kowa.

Ya ce Gwamnan Jihar Katsina ya umarce su da tabbatar da cewa an gudanar da rabon tallafin cikin adalci, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar wanda zai amfana ba.

Ya ƙara da cewa waɗanda ba su ga sunayensu a cikin jerin masu cin gajiyar shirin ba, kada su damu, domin nan ba da jimawa ba za a samu damar ganin sunayen wasu sabbin masu cin gajiyar shirin.

Shugaban shirin ya kuma yi kira ga duk wanda ya fuskanci matsala yayin rabon tallafin da ya tuntuɓi shugaban shirin na ƙaramar hukumarsa ko mataimakansa domin samun taimako.

Ya buƙaci waɗanda za su amfana da shirin da su ba jami’an da ke gudanar da rabon tallafin haɗin kai da goyon baya, tare da bin dokoki da ƙa’idojin da aka gindaya.

Aminu Alhassan ya kuma bayyana cewa an raba kuɗaɗen tallafin zuwa matakai uku. Akwai waɗanda za su karɓi kashi ɗaya, akwai masu kashi biyu, sannan akwai waɗanda za su karɓi kashi uku.

Ya ce waɗanda suka karɓi kashi ɗaya za a ƙara musu wani kaso daga baya, haka kuma waɗanda suka karɓi kaso biyu za a cika musu kaso na uku, yayin da waɗanda suka karɓi kaso uku suka kammala rabonsu.

Ya ƙara da cewa an tanadi tsari na musamman wajen karɓar kuɗin domin kare masu cin gajiyar shirin daga cuta, cin zarafi ko zalunci.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, Yahaya Ado, ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar Katsina da Shugaban Shirin tare da mataimakansa, inda ya bayyana cewa za su ci gaba da goyon bayan gwamnati.

By ukarofi