Mutane 150 sun sauya sheƙa zuwa APC a Dawakin Kudu

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Kimanin mutane 150 ne suka sauya sheka daga wasu jam’iyyu daban-daban zuwa jam’iyyar APC a ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu ta Jihar Kano.

Masu sauya shekar sun bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a Dawakin Kudu, inda suka ce sun yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne bisa la’akari da irin manufofi da shirye-shiryen jam’iyyar na kawo ci gaba da kyautata rayuwar al’umma.

Sauya shekar ta gudana ne ƙarƙashin jagorancin ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Alhaji Yusuf Datti Husaini Dawaki, wanda ya karɓi sabbin mambobin tare da tabbatar musu da cewa za su samu kulawa da goyon baya a cikin jam’iyyar.

Da yake jawabi, Jagoran APC na yankin, Alhaji Rabiu Nagwaggo Gano, ya yi maraba da sabbin mambobin, yana mai cewa shigarsu APC zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi da haɗin kai a yankin.

Ya kuma buƙaci sabbin mambobin da su kasance masu biyayya da kishin jam’iyya, tare da yin aiki tukuru domin samun nasarar APC a matakai daban-daban.

ɗaya daga cikin waɗanda suka sauya sheka, Dan Alhaji Kofar Gabas, ya bayyana cewa sun yanke shawarar shiga APC ne saboda amincewa da jagoranci da kuma ayyukan da ake ƙoƙarin aiwatarwa domin ci gaban al’umma.

Ya kuma tabbatar da cewa shi da sauran waɗanda suka sauya shekar za su yi aiki tare da sauran ’yan jam’iyyar domin tabbatar da nasarar APC a ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu.

A nasa bangaren, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Alhaji Yusuf Datti Husaini Dawaki, ya yi alkawarin ci gaba da sauraron buƙatun al’ummar yankin da yake wakilta, tare da ƙoƙarin samar musu da ayyukan ci gaba a dukkan mazabun yankin yadda ya kamata.

By ukarofi

Leave a Reply