Hajjin 2027: NAHCON ta bayyana dalilin rashin samun isassun gurbi ga masu adashin gata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ce tana sane da rashin jin daɗin waɗanda suka shiga tsarin adashin gata na HSS don zuwa aikin hajji kuma ba su samu gurbi ba acikin masu niyyar zuwa hajjin 2027. Ta kuma yaba da haƙurinsu, sadaukarwa da ƙoƙarinsu wajen son sauke ɗaya daga cikin wajiban addini.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun Kakakinta Mohammed Shafi’i Sani, ta ce Nijeriya kamar sauran ƙasashe, ta fuskanci ƙalubalen rage guraben hajji daga hukumomin Saudiyya saboda ƙarancinsu. A sakamakon haka, al’amarin ya shafi waɗanda suka shiga tsarin HSS, hukumomin jigilar alhazan jihohi, hukumomi da wasu masu niyyar zuwa hajjin na 2027.

Ya bayyana cewa, NAHCON za ta yi aiki ne bisa adadin gurbin da aka amince da kuma lokacin da aka ɗiba mata. Saidai hukumar ta ce tana maraba da matakin zuba jari a harkokin hajji daga ɓangaren gwamnatin Saudiyya da kuma fatan samun ƙarin wasu gurabe a nan gaba.

Adashin gata na Hajj Savings Scheme tsari ne na ajiya da shirin zuba jari ga masu niyyar zuwa aikin hajji don ba su biya da kaɗan-kaɗan ta yadda za su amfana daga hakan wajen samun gurbi, saidai hakan ba ya tabbatar da samun gurbi a wani zango na zuwa hajji.

Kazalika, NAHCON ta ce waɗanda hakan ya shafa za su iya neman a mayar musu da kuɗaɗensu ta bankunan da suka biya ko kuma jingine su zuwa hajjin 2028, matakin da ka iya taimakawa wajen samun rangwamen kuɗaɗen hidimar hajji. A cewar hukumar, tana aiki da hukumomi masu ruwa da tsaki wajen inganta harkokinta don walwalar alhazai.

By Babaji