A daina yaɗa bayanan ƙarya kan sabbin shugabannin APC

Daga SADIQ ABDULLATIF

A duk lokacin da aka saki wani bayani, galibi ba mu cika damuwa da bincikar sahihancin bayanin ba kafin yaɗawa. Wannan kuwa, na ɗaya daga ciki ƙalubalan soshiyal midiya da kafafen yaɗa labarai na zamani.

Don haka, na shigo ne domin in taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen fahimtar abubuwan da ke tattare da babban taron jam’iyyar APC da ya gudana kwanan nan. Kuma ina yin hakan ne da kyakkyawar niyya don faɗakar da mu da kuma ɗora komai a mizani a matsayina na tsohon Editan Labarun Siyasa.

Da farko dai ba gaskiya ba ne cewa an miƙa shugabancin APC ga jam’iyyar PDP.

A iya fahimtata, duk da dai gaskiya ne cewa sabon shugabancin APC ya samo tushensa ne daga PDP kasancewar sabon shugaban na APC tare da wasu sanatocin PDP su 10, sun sauya sheƙa ne zuwa APC a ranar 29 ga Janairun 2014, amma duk da haka yana daga cikin ginshiƙan APC tun bayan kafuwarta a Fabrairun 2013. A wannan lokacin ma, babu wani zaɓe da APCn ta lashe.

Wannan al’amari ya bambanta da abin da ya auku a PDP a Fabrairun 2016, inda aka ɗora mutumin da bai ma gama rufa shekara guda ba a a cikinta a matsayin shugaban jam’iyya. Wannan kuwa ya faru ne a daidai lokacin da sabon shugaban APC na yanzu ya yi haramar komawa APC.

Amma a wannan batu, Sanata Adamu ya shafe shekara takwas daga cikin shekaru taran da APC ta yi da kafuwa ana damawa da shi a cikinta. Wannan shi ne abu na farko.

Abu na biyu, shi ma Sakataren APC na ƙasa, Iyiola Omisore, ya samo asalinsa ne daga jam’iyyar ‘Alliance for Democracy’ (AD), inda aka soma zaɓen shi a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Osun. Kasancewar a wani lokaci ya sauya sheƙa ya zuwa PDP, hakan bai sanya shi zama cikakken ɗan jam’iyyar ta PDPn ba.

Hasali ma, mataimakan shugaban jam’iyya biyu da aka samu daga shiyyar Arewa da Kudu, wato Sanata Abubakar Kyari da Chief Emma Eneukwu, ba su da wata alaƙa da PDP. A cikin jam’iyyar APP suka soma siyasarsu har zuwa lokacin da aka yi maja ta koma APC.

Shi kuwa sabon Sakataren Tsare-tsare na APC, Suleiman Argungu, wanda ya kasance abokina, a baya shi ne shugaban Ƙungiyar Kare Martabar ANPP, wanda a wancan lokaci suka yi faɗi tashin ganin sun inganta jam’iyyar a lokacin da suke ganin PDP mai mulki ta mamaye komai. Kamar dai mataimakan shugaban jam’iyya, shi ma bai taɓa mu’amala da PDP ba.

Don haka, kada ku agaza musu wajen yaɗa bayanan bogi kan cewa an miƙa APC ga PDP, wannan ba gaskiya ba ne.

Wasu marubutan suna amfani da wannan damar ce sanin irin raunin da wasu masu karatu ke da shi na yarda da duk abin da suka karanta ba tare da sun yi tambaya ko bincike ba.

Sai dai irin waɗannan marubutan sun manta cewa wayon ‘yan Nijeriya ya wuce yadda suke tunani.

Sadiq ɗan jarida ne wanda ya rubuto daga Abuja, Bashir Isah ya fassara.