Tsadar abincin kifi zai haddasa rashin sa a Ramadan – PFFAN

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano 

Ma su sana’ar kiwon kifi sun koka kan yadda kamfanonin sarrafa abincin kifi ke tsawwala farashin kayan abincin kifi, inda suka bayyana cewa hakan zai iya kawo matsanancin tsadar kifi a watan Ramadan mai zuwa.

Wannan koke ya fito ne daga bakin shugabannin ƙungiyar masu sana`ar kiwon kifi a Nijeriya na ƙasa reshen Jihar Kano, wato Piratic Farmers Fish Association Of Nigeria, PFFAN a lokacin taron ƙungiyar da suka gabatar a Kano cikin makon jiya.

Hudu Salisu Khalid, shi ne kakakin ƙungiyar ta PFFAN, ya ce suna fuskantar ƙalubale da matsaloli masu yawa a wannan sana`ar, inda ya bayyana yadda kamfanonin sarrafa abincin kifi ke tsananin tsawwala farashin kaya a yanzu.

Kakakin ƙungiyar ya ce masu sayen kifi a wajen su, sun fi su cin riba idan suka sayar, inda ya ce su idan suka kiwata kifi tsawon wata shida ba ya wuce su ci ribar Naira 100 a kowane kilo, yayin da masu saye a wajen su ke cin fiye da Naira 300 a kowane kilo.

Hudu ya jingina wannan matsala ga su kamfanonin da ke sarrafa abincin kifi, inda a kusan kullum sai sun ƙara wa abincin farashi, inji shi.

Shi kuwa Isah Idris Muƙƙadas ya ce kiransu da gwamnatin Kano ƙarƙashin maaikatar gona da sauran masu ruwa da tsaki da su kawo agaji na ɗaukar matakan daƙile tsawwala farashi da kamfanonin abincin ke yi domun in ba haka ba duban ɗaruruwan matasa za su rasa aiki idan wannan sanaa tasu ta durƙushe.

Don haka akwai buƙatar ‘yan kasuwa su zo su kafa irin waɗannan kamfanoni domin rashinsu ne ke kawo wannan matsala duk da kayan sarafawan na rage farashi su kuma suna ƙara farashi. 

Shi kuwa Alhaji Yakubu Ibrahim Albarka, ɗaya daga cikin shugabanni masu wannan sana`a ta sayar da kayan abincin kifi da kaji da ke Kano, ya ce wannan ƙarin farashi ya samo asali ne daga ƙarin farashin masara, waken suya, tunkuza da sauran sinadaran da ake shigo da su daga waje wanda kowa ya san yadda Dala ta yi tashin gauran zabi.

Ga kuma matsalar man Diesel da sauransu ta yadda idan wani abu ya sauko a cikin kayan wani kuma ya yi tashi to wannan shi ne dai matsalar da muka samu kanmu a ciki. Inda wasu takwarorinsa a wannan sana`a ta siyar da abincin kifi da kaji suka yi gum kan wannan lamari.