A mayar da tsohon mataimakin gwamnan Zamfara Mahdi da aka tsige kujerarsa – Kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada umarnin mayar da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara wanda aka tsige, wato Mahadi Aliyu Gusau kan kujerarsa.

Mahadi dai shi ne Mataimakin Gwamna zamanin mulkin tsohon Gwamna Bello Matawalle, wanda aka tsige saboda ya ƙi bin shi Jam’iyyar APC daga PDP.

Mahadi da PDP ne suka shigar da ƙarar suna ƙalubalantar tsige shi da Majalisar Dokokin Jihar ta yi a watan Fabrairun 2022.

Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, Alƙalin kotun, Mai Shari’a Inyang ya ce matakin da tsohon Gwamna Matawalle da kwamitin binciken da ya kafa wanda ya kai ga tsige Mahadin raini ne ga batun da a lokacin yake gaban kotu.

Alƙalin ya ce, “Muna bayar da umarnin a dawo da wanda yake ƙara (Mahadi Aliyu Gusau) kan kujerarsa a matsayin Mataimakin Gwamnan Zamfara tun daga ranar 8 ga watan Yulin 2021 zuwa lokacin da aka shigar da wannan ƙarar.

“Kotu ta kuma jingine duk wani mataki da waɗanda aka yi ƙara suka ɗauka a kan batun tsige tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara, lokacin da ake wannan shari’ar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *