A shirye nake mu haɗu a kotu, martanin Tinubu ga Atiku

Daga BASHIR ISAH

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Ahmed Tinubu, ya ce a shirye yake su fafata a kotu tare da ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, kan ƙarar da ya ce zai shigar.

Da yake jawabi yayin taron manema labarai a ranar Alhamis, Atiku ya yi zargin ba a yi adalci ba a zaɓen da ya gudana Asabar da ta gabata wanda hukumar INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara.

Da yake maida martani ta bakin Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, Festus Keyamo (SAN), Tinubau ya ce, “A shirye yake wa ƙalubalantar sakamakon zaɓen da Atiku ya ce zai yi.

“A shirye muke mu fuskance shi a ko’ina a kuma kowane lokaci.

“Muddin Atiku Abubakar da sauran ‘yan takarar da suka sha kaye ba su yarda da tayin a tafi tare da Tinubu ya yi musu ba, ƙarƙarin abin da Atiku zai iya yi shi ne ya tattara komatsansa ya koma Dubai inda ya saba zama.

“Kamata ya yi Alhaji Atiku Abubakar ya gode kasancewar shi ne ya zo na biyu a zaɓen, duk da rigingimun da jam’iyyarsu ke fama da su….”

Tinubu ya ce Atiku Abubakar ya yi abubuwa da yawa da suka saɓa wa jam’iyyarsa, ciki har da saɓa wa tsarin karɓa-karɓa na jam’iyyar tasu da dai sauransu.