Abba Yusuf ya kai bantensa a Kotun Ƙoli

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kotun Koli ta battabar da nasarar da Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya samu a zaben 2023 a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kano.

A ranar Juma’a Kotun Kolin ta kawo karshen gardamar da ake yi tsakanin Abba Kabir da Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC dangane da shugabancin Jihar Kano.

Yayin yanke hukuncin, alkalan kotun sun tabbatar da cewa, Kotun Daukaka Karar ta yi rashin fahimta na soke kuri’u 165,616 na Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta yi.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya kuma bayyana cewa batun kasancewar Gwamna Yusuf ba dan jam’iyyar ba, wani lamari ne da ya kamata a yi shi gabanin zabe.

Kazalika, kotun ta ce batun tsayar da dan takara ko daukar nauyin zabe hakki ne na jam’iyya.

Tun  bayan kammala zaben gwamnan jihar a 2023 wanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, jam’iyyar APC da dan takararta Yusuf Gawuna, suka shigar da kara Kotun Sauraren Kararrakin Zabe inda suka kalubalanci sakamakon zaben.

Kafin wannan lokaci, Kotun Daukaka karat a soke nasarar da Abbab ya samu, lamarin da ya sa Abba da jam’iyyarsa ta NNPP suka garzaya Kotun Daukaka Kara don kare nasararsu.

By Editor