Rundunar sojoji ta kama jami’an da suka azabtar da fararen hula

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar Sojojin Nijeriya ta kama wasu jami’anta biyu bayan da wani bidiyo ya nuna suna azabtar da farar hula a Jihar Ribas.

Bidiyon wanda ya karade shafukan sada zumunta, ya nuna wani sanye da kakin soji da kuma wani cikin kayan farar hula suna azabtar da wani mutum, duk da hakuri da ya yi ta ba su.

Mutumin ya yi ta kuka yana fadin cewa, “A’a, don Allah ku yi hakuri, zan fadi gaskiya.”

Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ranar Laraba, ta nuna bacin ranta kan abin da jami’an biyu suka aikata inda ta ce ba za ta lamunci irin haka ba.

“Muna so mu tabbatar da cewa mun kama sojojin da suka aikata wannan abu na sava ka’idar aiki,” inji sanarwar.

Mutane da dama sun yi Allah-wadai da abin da jami’an sojin suka aikata bayan da bidiyon ya karade shafukan sada zumunta, inda wani mai amfani da shafin X ya kwatanta dabi’un sojojin da “Rashin imani da kuma sava ka’idar aiki”.

Sojojin sun tabbatar da cewa za su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da yin alkawarin hukunta wadanda suka aikata laifin.

A baya, kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasa da kasa sun sha sukar sojojin Najeriya kan zargin take ’yancin xan adam da ya hada da azabtarwa, tsarewa da kuma kashe-kashe ba bisa da’ida ba.

By Editor