Daga AMINA YUSUF ALI
Kamfanin mai na Shell ya fasa sayar da kadarorisa wato gine-gine sa da kayan aiki da yake da su a ƙasar nan.
Hakan ya biyo bayan bin umarnin kotun ƙolin da kamfanin ya yi bayan da mazauna garin Bayelsa suka ɗaukaka ƙara a kan kamfanin.
Babban kamfanin man ya bayyanana daina harkokin kasuwancinsa a Nijeriya a watan Mayun 2021. Daga bisani kuma al’ummar yankin Aghoro ƙaramar hukumar Ekeremor ta jihar Bayelsa ta shigar da kamfanin ƙara kan a biya su diyyar ɓarnar da yoyon fayif ɗin man kamfanin ya jawo wa al’ummar garin wanda ya faru ranar 17 ga watan Mayu, 2018.
A ranar 16 ga watan Yunin shekarar nan ta 2022 ne dai kotun ƙolin ta dakatar da kamfanin Shell daga sayar da kadarorinsa na Nijeriya har zuwa watan Oktoban shekarar nan. Wato har sai an warware taƙaddamar da take tsakanin su da al’ummar Niger Delta da suka nemi Kamfanin ya biya su diyyar Naira biliyan 700 fansa ga ɓarnar da yoyon man kamfanin ya yi musu.
A lokacin da kotun ta ba da umarnin, mai magana da yawun kamfanin ya bayyana cewa, sam umarnin kotun na ranar 16 ga watan Yuni, 2022 bai shafi dukkan kadarori kamfanin ba illa wasu daban. Amma duk da haka, ya amince da biyayya ga umarnin kotun.
A ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne dai Manajan darakta kuma Chiyaman na kamfanin Shell, Osagie Okunbor, ya sake bayyana cewa, kamfanin ba zai cigaba da ƙudurinsa na sayar da kadarorisa da suke Nijeriya ba har sai an sanar da hukuncin ƙarar da aka ɗaukaka a kan kamfanin. Domin a cewar sa, kamfanin ya kasance mai girmamawa da bin dokar Shari’a tare da bin umarnin kowanne kotu a Nijeriya.