Matsin tattalin arziki ya hana mutane da dama sayen ragunan layya bana a Zariya

Daga MOHD BELLO HABIB a Zariya

Sakamakon matsin tattalin arziki ya hana wasu jama’a da dama sayen ragunan layya bana saboda tsadar da dabbobin suka yi.

Da yake zantawa da wakilin Manhaja a Zariya jiya akan farashin dabbobin a bana, dillalin dabbobi da ke Zariya, Alhaji Abdulmumini Alhassan Sarkin Turken Zazzau ya koka akan tsadar da dabbobin suka yi a bana, ya ce kasuwar ba ta tafiya kamar yadda aka saba.

Ya ce, qaracin kuɗi a hannu jama’a ya sanya cinikin dabbobin ya tsaya cak, ya ƙara da cewa ga dabbobin jibge amma babu masu saye saboda tsadarsu.

Sarkin Turken ya ce ragon da aka saye shi bara akan Naira dubu 30 a bana ana sayar da shi ne akan Naira dubu 70 ko fiye da haka wanda aka saye a Naira dubu 50 a bara yanzu shi ne dubu 120 zuwa dubu 140, ya ce a bana layya sai dai wane da wane ba kamar shekurun baya.

Alhaji ya danganta tsadar dabbobin da ƙarancinsu saboda matsalar tsaro da yawan sace-sacen su da ake yi gami da tsadar safarar dabbobin.

Ya ce a bara suna biyan kuɗin motar dake kwaso dabbobin daga jihohin kamar su Kano da Jigawa da Katsina akan Naira dubu 40 to amma yanzu sukan biya dubu 120 ne zuwa Zariya.

Dangane da yadda suke jigbe a kara, ya ce wasu waɗanda suka sayi dabbobin kan bar su ne a wajen sai ranar Sallah su ɗauka saboda rashin wajen ajiya da kuma tsaro.